Allah ya yi wa tsohuwar jarumar Kannywood, Zainab Booth rasuwa

Allah ya yi wa tsohuwar jarumar Kannywood, Zainab Booth rasuwa

  • Fitacciyar ‘yar wasan Hausa ta Kannywood, Hajiya Zainab Booth ta rasu
  • Hajiya Zainab ta amsa kiran mahaliccinta a daren ranar Alhamis, 1 ga watan Yuli
  • Za a yi jana'izarta a safiyar yau Juma'a, 2 ga watan Yuli da misalin karfe 8:00am

Allah Ya yi wa fitacciyar tsohuwar jarumar masana’antar shirya fina-finan Hausa ta Kannywood, Hajiya Zainab Musa Booth rasuwa.

Zainab Booth ta rasu ne a daren ranar Alhamis, 1 ga watan Yuli a jihar Kano.

KU KARANTA KUMA: Gwamnan Najeriya ya yi hasashen watan da za a yi gagarumin sauye-sauyen sheka a APC da PDP

Allah ya yi wa tsohuwar jarumar Kannywood, Zainab Booth rasuwa
Zainab Booth ta rasu a daren ranar Alhamis, 1 ga watan Yuni Hoto: realalinuhu
Asali: Instagram

Marigayiyar ita ce mahaifiyar shahararrun ’yan wasan Hausa uku wato Maryam Booth, Ramadan Booth da kuma Amude Booth.

Za a yi jana’izarta a safiyar yau Juma’a, 2 ga watan Yuli, da misalin karfe 8:00 a gidanta da ke kallon Premiere Hospital a Court Road, kamar yadda jarumi Ali Nuhu ya wallafa a shafinsa na Instagram.

KU KARANTA KUMA: Waiwaye: Tsoffin hotunan tsohon Shugaban kasa Obasanjo da ke nuna shi jakadan Najeriya ne na kwarai

Jaruma Maryam Booth ma ta sanar da rasuwar mahaifiyar tata a shafinsa na Instagaram.

Ta rubuta a shafin nata:

“Innalillahi wa’inna illaihi raji’un. Allah yayi ma mahaifiyata rasuwa za akaita gobe Juma’a da safe 8ama.
“Address premier clinic court road zoo road kano. Allah Mata rahama yasa annabi yasan da zuwanta.”

Tuni masoya suka fara mika sakonninsu na ta’aziyya

Mabiya shafin Instaram sun yi tururuwa wajen aika sakon ta'aziyya da jaje ga iyalan.

humayyrahh ta yi addu’an:

“Allah ya jikan ta ..Allah yasa ta huta..Allah yayi mata rahama.Aameen ❤️kada ki karaya.”

ummizeezee ta ce:

“Allah ya ji kan ki mama.”

h_h_collections_lagos ta rubuta:

“Allah yayi mata Rahama.”

asmautripple_a ta ce

“Allah ya jikan ta da rahama.”

Allah yayi wa zukekiyar jarumar Kannywood, Khadija Mahmud, rasuwa

A wani labarin, Legit.ng ta kawo a baya cewa Allah da girma yake! Allah ya tabbatar mana da cewa dukkan rai zai dandana mutuwa.

A safiyar Alhamis, 6 ga watan Mayun 2021 ne jaruma Khadija Mahmud ta masana'antar Kannywood ta amsa kiran mahaliccinta.

Jarumar ta rasu a garin Jalingo na jihar Taraba wurin karfe 6 na safe yayin da take hannun mahaifiyarta suna hanyar zuwa asibiti.

Asali: Legit.ng

Online view pixel