Jaruman Kannywood 12 da Taurarinsu suka fi haskawa a 2021

Jaruman Kannywood 12 da Taurarinsu suka fi haskawa a 2021

Masana'antar Kannywood dai na kunshe ne da jarumai masu tarin yawa. Akwai tsoffin jarumai, sabbi da kuma masu tasowa. Wasu sun yi suna ne a wannan shekarar sakamakon rawar da suke takawa a wasu fina-finai masu dogon zango.

A cikin shekarar nan ta 2021, akwai jaruman da tauraruwarsu ta fi haskawa sakamakon wata rawa da suka taka a wasu sabbin fina-finai ko kuma makamancin hakan.

Legit.ng ta tattaro wa masu karatu jerin jaruman Kannywood 12 da tauraruwarsu ta fi haskawa a wannan shekarar.

1. Lawan Ahmad

Wannan dai tsohon jarumi ne kuma ba tun yanzu ba masu kallon fina-finai suka fara ganinsa. Lawan Ahmad ya samu shuhura ne sakamakon fim din sa na wannan shekarar mai suna Izzar so. Babu shakka wannan yasa ya samu karbuwa a wurin jama'a.

Kara karanta wannan

Mai yankan kauna: Rasuwar angon Disamba ta tada hankulan ma'abota Facebook

Jaruman Kannywood 12 da Taurarinsu suka fi haskawa a 2021
Jaruman Kannywood 12 da Taurarinsu suka fi haskawa a 2021. Hoto daga hutudole.com
Asali: UGC

Shin kana da labarin da ka/ki ke son an wallafa ma ka/ki? Ka tuntubemu a info@corp.legit.ng!

2. Adam Abdullahi Adam, wanda aka fi sani da Daddy Hikima ko Abale

Abale ya kasance ma'aikacin jinya ne kafin ya shigo masana'antar. Tauraruwarsa ta fara haskawa ne a wani fim mai dogon zango mai suna A Duniya.

A halin yanzu Daddy Hikima shi ne ke jan ragamar fin din Sanda da Na Ladidi. A yanzu haka Abale ya na bayyana a fim mai dogon zango na Labari na.

3. Ummi Rahab

An haifa jaruma Ummi Rahab a shekarar 2004. Ta fara bayyana a wani tsohon fim mai suna Ummi. Tauraron ta ya hasko a wannan shekarar bayan ta fara fim din farin wata kafin daga bisani ta fara fim mai dogon zango mai suna Wuff na mawaki mai suna Lilin Baba.

4. Aisha Najamu

Jaruma Aisha Najamu ta fara bayyana ne a shekarar nan a cikin shiri mai dogon zango mai suna Izzar so. Salon takamar ta da nuna isa ne yasa jama'a ke son wasan ta.

Kara karanta wannan

Kafa Ƙasar Biafra Da Oduduwa: Tsohon Mai Neman Takarar Shugaban Ƙasa Daga Arewa Ya Goyi Bayan Kanu da Igboho

5. Nuhu Abdullahi

Wannan tsohon jarumi ne amma tauraruwarsa ba ta haska ba har sai a wannan shekarar bayan bayyanarsa a fim mai dogon zango mai suna Labarina inda ya fito a matsayin Mahmud.

6. Rabiu Rikadawa

Wannan tsohon jarumi ne kuma tuntuni ya shahara. Sunansa ya bayyana kuma ya sake fitowa ne a shiri mai dogon zango na Labarina inda ya fito matsayin Baban Dan Audu.

Babu shakka salon da ya bayyana da shi na damfara, son abun duniya da kuma yadda ya saje da wannan bangaren ya kawatar da masu kallo.

7. Abdul M. Shariff

Jarumi Abdul M Sharif ya fito a cikin shirin Wuff, A Duniya da kuma Da a ce ba Zuciya. Jarumin ya kasance shahararren jarumin da tauraronsa ke haskawa a cikin wadannan fina-finai na shekarar nan.

8. Nafisa Abdullahi

Jaruma Nafisa Abdullahi dai ba sabuwar jaruma bace. Ta dade ta na gwagwarmaya a masana'antar. Sai dai a wannan shekarar, sunan ta ya fi fitowa tare da haskawa sakamakon rawar da ta ke takawa a fim mai dogon zango mai suna Labarina.

Kara karanta wannan

Kudi na magana: Masoya sun tarawa Davido sama da Naira miliyan 120 a ‘yan awanni

9. Hauwa Ayawa

Wannan jaruma dai za mu iya cewa a wannan shekarar ne ta fara haskawa kuma an fi sanin ta da suna Aziman Gidan Badamasi, fim mai dogon zango da ya fito da ita a wannan shekarar.

10. Tijjani Asase

Wannan jarumin ya dade a masana'antar Kannywood kuma ya bayyana a fina-finai daban-daban. Sai dai jarumin ya yi shuhura a wannan shekarar ne sakamakon rawar da ya ke takawa a fim din Gidan Badamasi da A Duniya.

11. Shamsu Dan Iya

Duk da ba wannan bace shekarar farko da jarumin ya fara yin suna ba, sunan shi ya sake fita ne a fim din Bana Bakwai da kuma Gargada.

12. Momy Gombe

Babu shakka wannan jarumar ta yi suna a wannan shekarar sakamakon fina-finan da ta ke fitowa tare da manyan jarumai. Ta kan fito tare da manyan jarumai kamar su Ali Nuhu, Adam Zango da sauransu.

Kara karanta wannan

Albashi ba adadi: Abubuwa 6 da ya kamata ku sani game da limamin Harami, Sheikh Sudais

Asali: Legit.ng

Online view pixel