Da duminsa: Allah ya yiwa jarumin Kannywood Sani Garba SK rasuwa

Da duminsa: Allah ya yiwa jarumin Kannywood Sani Garba SK rasuwa

Jihar Kano - Allah Ya yi wa fitaccen ɗan wasan fina-finan Hausa na masana'antar Kannywood Sani Garba wanda aka fi sani da Sani SK rasuwa

BBC Hausa ta ruwaito cewa jarumin ya rasu ne a yau Laraba a birnin Kano, bayan doguwar jinyar da yayi.

Rahoton yace fitaccen furodusa Abdul M Amart Mai Kwashewa ne ya tabbatar da rasuwar ɗan wasan.

Yace marigayin ya rasu ne a Asibitin Muhammadu Abdullahi Wase da ke Nasarawa.

Yace:

"Sani SK ya kai kusan shekara uku yana jinya a tsattsaye, amma rashin lafiyar ta taso masa sosai ne a baya-bayan nan inda ya shafe mako biyar yana jinya a asibitin."

Shin kana da labarin da ka/ki ke son an wallafa ma ka/ki? Ka tuntubemu a info@corp.legit.ng!

Kara karanta wannan

Labari mai dadi: Shugaba Buhari ya kara wani kaso mai tsoka a albashin 'yan sanda

Da duminsa: Allah ya yiwa jarumin Kannywood Sani Garba SK rasuwa
Da duminsa: Allah ya yiwa jarumin Kannywood Sani Garba SK rasuwa
Asali: UGC

Asali: Legit.ng

Tags:
Online view pixel