‘Yan bindiga sun fito da Malaman musuluncin da suka sace bayan an biya fiye da Naira miliyan 2

‘Yan bindiga sun fito da Malaman musuluncin da suka sace bayan an biya fiye da Naira miliyan 2

A ranar Asabar da ta wuce ne Miyagun ‘yan bindiga suka yi garkuwa da wasu malamai a Ayetoro

Bayan kwana uku a hannun ‘yan bindiga, an biya N2.2m, an yi nasarar kubuto da wadannan malamai

Jami’an 'yan sandan da ke Ogun sun gagara ceto Sheikh Hussein AbdulJelil da Ilyas Muhammed Jamiu

Ogun – Miyagun ‘yan bindigan da suka sace malaman addini a garin Ayetoro, karamar hukumar Yewa ta Arewa, jihar Ogun, sun fito da su bayan an biya kudi.

A ranar 22 ga watan Disamba, 2021, Daily Trust ta rahoto cewa Hussein AbdulJelil da Ilyas Muhammed Jamiu sun samu ‘yanci bayan an biya kudin fansa.

Kamar yadda rahoton ya bayyana, ‘yanuwan wadannan malamai sun bada Naira miliyan 2.2 kafin su fito. Da farko an bukaci ‘yanuwan su kawo Naira miliyan 15.

Kara karanta wannan

Tashin hankali yayin da 'yan bindiga sun sace sarkin gargajiya da malamin fada

A karshe masu garkuwan suka yarda su karbi N2.2m. An yi awon gaba da wadannan shehunnai ne a kan hanyarsu ta dawowa daga wajen darasin addini a Yewa.

‘Yanuwa da abokan arziki sun yi yunkurin kai lamarin wajen jami’an tsaro, amma ba ayi nasarar cafke wadanda suka yi garkuwa da wadannan malaman biyu ba.

Yan sanda
Jami'an Yan sanda Hoto: @PoliceNG/Twitter
Asali: Twitter

Punch tace ana zargin ‘yan bindiga biyar suka yi gaba da Hussein AbdulJelil da Ilyas Jamiu. Lamarin ya faru a ranar Asabar da ta gabata da karfe 10:00 na dare.

Labarin fitowarsu a ranar Talata

Daya daga cikin ‘yanuwan wadanda aka dauka, Hussein Ibrahim ya tabbatar da labarin kubutarsu, inda yace ‘yanuwa da abokai ne suka hada kudin fansar.

“An sake su a yau (Talata, 21 ga watan Disamba, 2021) bayan mun biya su Naira miliyan 2.2 a matsayin kudin fansa.”

Kara karanta wannan

Nasara: Sojoji sun ragargaji sansanin dan bindiga Bello Turji, sun hallaka da dama

“Da fari sun hakikance a kan sai an biya N15m tun da mutane biyu suka dauke, a karshe su hakura, suka karbi N2.2m.”
- Hussein Ibrahim

Ina jam'in tsaro?

Da aka tuntubi kakakin ‘yan sanda na jihar Ogun, Abimbola Oyeyemi, ya bayyana cewa bai san da labarin ba, yace ba a sanar da shi game da kubutar malaman ba.

Mutuwar Bola Ige SAN

Dazu aka ji cewa a Disamban shekarar 2001, wasu mutane su ka je har gidan Bola Ige ya na Ministan tarayya, su ka buda masa wuta, shekaru 20 kenan a yau.

Mutane na so a tona asirin wadanda suka kashe gawurtaccen ‘dan siyasa kuma kwararren lauyan. Farfesa nan, Wole Soyinka yana cikin masu wannan kira.

Asali: Legit.ng

Online view pixel