Yanzu Yanzu: Allah ya yi wa jarumin Kannywood, Ahmad Tage rasuwa

Yanzu Yanzu: Allah ya yi wa jarumin Kannywood, Ahmad Tage rasuwa

  • Jod, Alhaji Aliyu Ahmad Tage ya rasu
  • Ahmad Tage ya amsa kiran mahaliccinsa a yau Litinin, 13 ga watan Satumba
  • Ya rasu sakamakon gajeruwar rashin lafiya da ya yi ta fama da ita

Kano - Allah Ya yi wa fitaccen jarumi kuma mai daukar hoto a masana’antar shirya fina-finan Hausa ta Kannywood, Alhaji Aliyu Ahmad Tage rasuwa.

Ahmad Tage ya rasu ne a ranar Litinin, 13 ga watan Satumba a jihar Kano bayan ya yi fama da yar gajeruwar rashin lafiya.

Yanzu Yanzu: Allah ya yi wa jarumin Kannywood, Ahmad Tage rasuwa
Allah ya yi wa jarumin Kannywood, Ahmad Tage rasuwa Hoto: ayatullahi_tage
Asali: Instagram

Jarumin ya fito a cikin fina-finai da dama kuma ya yi suna ne a cikin fina-finan barkwanci na marigayi Rabilu Musa Dan Ibro.

Tuni jaruman Kannywood suka tabbatar da mutuwar tasa tare da yi masa addu’ar samun jin Kan Ubangiji a shafukansu na sadarwa.

Kara karanta wannan

Ministoci 13 da ya kamata Shugaban kasa Buhari ya fatattaka daga Gwamnatinsa

Shin kana da labarin da ka/ki ke son an wallafa ma ka/ki? Ka tuntubemu a info@corp.legit.ng!

Jarumar Kannywood, Saratu Gidado da aka fi sani da Daso ta wallafa a shafinta na Instagram:

“Innalillah wa inna ilaihi raji'uun. Kannywood munyi rashin Director/Actor/Camera Man Alh.Aliyu Ahmad Tage yau Litinin 13/09/2021 Allah ya karbi abinsa. Ya fito a fina finai da dama. Ciki harda Film din NA MAMAJO,inda yakewa Marigayi IBRO Wuuuu ai se bayan kwana 2.
“Allah yajikansa yayi masa rahma. Allah ya kyauta tamu karshen.”

Ali Nuhu ma ya wallafa a shafinsa:

“Inna Lillahi Wa'inna Ilaihi Raji'un. Allah ya yi wa daya daga cikin masu daukar hoto kuma jarumi a masana'antar Kannywood, Ahmad Tage rasuwa.
“Ya rasu sakamakon gajeruwar rashin lafiya da ya yi ta fama da ita. Muna rokon Allah ya jikansa da rahama.”

Jama'a sun nuna alhini tare da yi masa addu'a

ayshatulhumairah ta yi masa addu'a:

Kara karanta wannan

Buhari: Gwamnan Ebonyi ya yi wa Wike raddi, ya fallasa wadanda suka kawo matsalar tsaro

"Allah ya gafarta masa yasa mutuwa Hutu ce a gare ya kyautata Karshen Mu "

mustapha_badaru ya yi sharhi:

"Allah yajikanshi"

umargombe ya rubuta:

"Innalillahi wa'inna ilaihir raji'un!"

Allah ya yi wa tsohuwar jarumar Kannywood, Zainab Booth rasuwa

A yan watanni da suka gabata mun kawo batun rashi da masana'atar tayi na fitacciyar tsohuwar jaruma, Hajiya Zainab Musa Booth.

Zainab Booth ta rasu ne a daren ranar Alhamis, 1 ga watan Yuli a jihar Kano.

Marigayiyar ita ce mahaifiyar shahararrun ’yan wasan Hausa uku wato Maryam Booth, Ramadan Booth da kuma Amude Booth.

Asali: Legit.ng

Online view pixel