Kai dai mai cika alkawari ne: Sarkin Daura ya yabawa mataimakin Buhari, Yemi Osinbajo

Kai dai mai cika alkawari ne: Sarkin Daura ya yabawa mataimakin Buhari, Yemi Osinbajo

  • Jama'a da dama sun cika kan titin sun tarbi mataimakin shugaban kasa Farfesa Yemi Osinbajo zuwa Daura ta jihar Katsina
  • Mataimakin shugaban kasa Osinbajo ya dura ne a wurin da aka gudanar da bikin nadin sarautar Yusuf Buhari a matsayin Talban Daura
  • Bisa ga bikin nadin da aka masa, dan shugaban kasa, Yusuf Buhari ya samu matsayi a masarautar garin mahaifinsa, Daura

Daura, Katsina - Sarkin Daura, Dr. Umar Farouk Umar a ranar Asabar, 18 ga watan Disamba ya yabi mataimakin shugaban kasa Farfesa Yemi Osinbajo.

Mataimakin shugaban kasa Osinbajo ya halarci nadin dan shugaban kasa Muhammadu Buhari, Yusuf, a matsayin Talban Daura, hakimin gundumar a jihar Katsina.

Farfesa Yemi Osinbajo da Buhari
Kai dai mai cika alkawuri ne: Sarkin Daura ya yabawa mataimakin Buhari, Yemi Osinbajo | Hoto: Buhari Sallau
Asali: Twitter

A rahoton da Legit.ng ta tattaro daga masarautar, ta ce lokacin da sarkin da magana game da mataimakin shugaban kasa, Sarkin Daura ya ce:

Kara karanta wannan

Fadar Shugaban kasa ta jero tulin nasarorin Shugaba Buhari yayin da ya cika shekara 79

“Muna mika godiyarmu ga mai martaba, wakilin shugaban kasa. Shi mataimakin shugaban kasa mutum ne mai martaba mai cika alkawuran da ya dauka kuma amintacce ne mai hakuri da sanin abin da ya dace a kowane lokaci.”

Shin kana da labarin da ka/ki ke son an wallafa ma ka/ki? Ka tuntubemu a info@corp.legit.ng!

Da yake bayyana matsayin Osinbajo a wurinsa, sarkin ya kara da cewa:

“Mutumin kirki ne, mutum ne da nake so amma na kan manta yadda zan furta sunansa yadda ya kamata. Mutum ne mai kirki na kwarai.”

Bayan da aka nada dan shugaban kasa, Sarkin ya bayyana cewa nadin nasa shine:

"Nuna godiya ga shugaban kasa Muhammadu Buhari."

Ya kara da cewa:

“Masarautar ta yanke shawarar nunawa mai girma, Muhammadu Buhari alamar godiya daga garinsu.
“Ko da yake mun san cewa saboda shekarunsa ba zai iya zuwa gida ya karbi mukami na gargajiya ba, don haka muka roke shi ya ba mu dansa domin mu dora shi a matsayin hakimi a wani kaso da muka amince da shi a shata, a ba shi hakimin gunduma kuma mai mulkarta.

Kara karanta wannan

Sarkin Daura: Mun ba Yusuf Buhari sarauta ne don kada ya riƙa gararamba a Abuja bayan Buhari ya sauka mulki

“Ku shaida ’yan uwana masu mulki, ba ma ba wani mukami saboda tsoro ko wani abu, muna ba wanda zai taimaki sarki ya taimaka masa wajen mulkar talakawa a zuciyarsa.

Bayan mataimakin shugaban kasa Osinbajo, wasu manyan baki da suka halarci taron sun hada da gwamnonin jihohin Katsina da Kano; shugaban majalisar dattawa, Ahmad Lawan, mataimakin shugaban majalisar dattawa Ovie Omo-Agege, da wasu ‘yan majalisar wakilai da dama.

Haka kuma akwai mambobin majalisar zartarwa ta tarayya da suka hada da sakataren gwamnatin tarayya Boss Mustapha da wasu ministoci biyu.

Asagba na Asaba ya yabawa Osinbajo

A baya kadan, Basaraken gargajiyan Asaba na jihar Delta, Farfesa Chike Edozien, ya bayyana mataimakin shugaban kasa Osinbajo a matsayin haziki kuma babban mataimaki ga shugaba Buhari.

Asagba ya yi wannan tsokaci ne a ranar Litinin, 29 ga watan Nuwamba lokacin da mataimakin shugaban kasar ya kai masa ziyarar ban girma a garin Asaba.

Kara karanta wannan

Bayan da SSS suka fatattaki masu zanga-zanga a Katsina, Masari ya kai kara wajen Buhari

Mataimakin shugaban kasan ya ziyarci sarkin ne a wata ziyarar da ya kai don kaddamar da sabuwar sakateriyar ma’aikata ta jihar Delta, wanda kuma aka sanyawa sunan sarkin gargajiyar.

A wani labarin na daban, Sarkin Kano na yanzu, Alhaji Aminu Bayero, na daf da angwancewa da wata tsohuwar zumansa da aka bayyana da suna Hajiyayya da ke zaune a unguwar Dorayi da ke cikin birninsa Kano.

Sarkin wanda ke da mata daya tilo da ‘ya’ya har hudu, zai kara aure ne bayan shekaru talatin da auren matarsa ta farko da yake zaune da ita a ya halin yanzu.

Wasu majiyoyi da ke kusa da dangin sun shaidawa jaridar Daily Nigerian cewa ana ci ga da tsare-tsaren bikin a asirce tsakanin wakilan masarautar Kano da kuma danginsu amaryar.

Asali: Legit.ng

Online view pixel