Bayan da SSS suka fatattaki masu zanga-zanga a Katsina, Masari ya kai kara wajen Buhari

Bayan da SSS suka fatattaki masu zanga-zanga a Katsina, Masari ya kai kara wajen Buhari

  • Tun da farko dai wasu masu zanga-zangar sun bazama kan titunan jihar Katsina saboda nuna jimaminsu da tabarbarewar tsaro a yankin inda jami’an SSS da ‘yan sanda suka tarwatsa su
  • Bayan haka ne gwamnan jihar Katsina da wasu dattawa suka kai kara ga shugaban kasa a ranar Talata 14 ga watan Disamba
  • Gwamna Bello Masari bayan taron ya bayyana cewa akwai bukatar dukkanin jihohin yankin Arewa su hada kai, su tashi tsaye domin murkushe ‘yan fashin bindiga

Abuja - Biyo bayan yawaitar kashe-kashe a wasu sassan kasar nan, zanga-zanga ta mamaye titunan Abuja da jihar Katsina a ranar Talata 14 ga watan Disamba.

Kungiyar hadin kan Arewa ta yi taro a Unity Fountain da ke Abuja, inda ta yi zanga-zangar nuna rashin amincewa da hare-haren da ake kai wa a fadin kasar.

Kara karanta wannan

Rashin tsaro: Dattawan Katsina sun dura Abuja, sun gana da Shugaba Buhari a fadar Aso Villa

Shugaban kungiyar, Yahuza Getso, ya kuma nuna rashin jin dadinsa ga gwamnatin Shugaba Muhammadu Buhari.

Ganawar shugaba Buhari da gwamnan jihar Katsina
Bayan da SSS suka fatattaki masu zanga-zanga a Katsina, Masari ya kai kara wajen Buhari | Hoto: Buhari Sallau
Asali: Facebook

Ganin haka ne Gwamna Aminu Masari na jihar Katsina a jiya ya jagoranci tawagar dattawan jiharsa zuwa wata ganawar sirri da shugaban kasa Muhammadu Buhari a fadar shugaban kasa da ke, Abuja, kamar yadda jaridar Daily Trust ta ruwaito.

Su waye Dattawan?

Dattawan sun hada da Sanata Abba Ali (dan ajinsu Buhari a makaranta), Alhaji Aliyu Mohammed, Sanata Mamman A. Danmusa, Alh Nalado Y. Sarkin Sudan da Alhaji Ahmed Yusuf.

Gwamna Masari yayi jawabi ga manema labarai

Da yake yiwa manema labarai jawabi bayan kammala taron, Masari ya jaddada bukatar dukkanin jihohin Arewa maso Yamma su hada kai domin murkushe ‘yan bindiga, inji Vanguard.

Yace:

Kara karanta wannan

Hare-haren Sokoto: Duk laifin Jami'an Sojojin Najeriya ne, Gwamna Tambuwal

“Ina ganin abin da ya fi dacewa mu yi don yin nasara wajen yakar wadannan ‘yan bindiga shi ne dukkan jihohinmu, musamman ma jihohin Arewa maso Yamma, mu dauki bakin cikin da muke ciki, mu hada kai don ganin mun toshe duk wata rigima.
“Amma idan wata jiha tana da manufa kaza, wata kuma tana da wata manufa ta daban, to tabbas su ('yan bindiga) za su rika tafiya daga wannan jiha zuwa waccar.
"An yi sa’a, mun riga mun hada gwiwa da jahohin da ke kan iyaka da mu, kamar Nasarawa da Neja, don kawo matsalar zuwa matakin da za a iya shawo kan ta.”

Dangane da kisan da aka yi wa daya daga cikin kwamishinoninsa na baya-bayan nan, Masari ya ce lamarin ba shi da alaka da ‘yan bindiga, yana mai cewa lamarin kisan kai ne daga wadanda aka dauke su haya.

Masari ya lura cewa:

Kara karanta wannan

Matasa Sun Fita Gari Sunyi Zanga-Zanga Kan Yawaitar Kashe-Kashe a Arewa

“Idan muna maganar ‘yan bindiga ne, tabbas, mun ga an samu ci gaba; Ba za mu iya cewa an dawo daidai ba, amma akwai ci gaba."

DSS ta ce jama'a su kula, ana kokarin fara daukar dalibai aikin bindiganci da sace mutane

Hukumar tsaro ta farin kaya (DSS), ta jawo hankalin jama’a kan wani shirin daukar dalibai aikin ‘yan bindiga, garkuwa da mutane, fashi da makami dakuma laifukan satan kudi, kamar yadda jaridar Leadership ta ruwaito.

Kakakin hukumar ta DSS, Dr Peter Afunanya ne ya bayyana haka a wani taron manema labarai a Abuja ranar Talata 14 ga watan Disamba.

Hukumar ta DSS ta ce baya ga dalibai, ‘yan Majalisar Dokoki/Majalisun Jihohi da ke hutu da sauran ma’aikatan gwamnati da masu zaman kansu da ke hutu na iya fuskantar barazanar tsaro daban-daban.

Asali: Legit.ng

Online view pixel