Sarkin Kano zai angwance da galleliyar budurwa, tsohuwar zumansa nan kusa

Sarkin Kano zai angwance da galleliyar budurwa, tsohuwar zumansa nan kusa

  • Sarkin Kano, Alhaji Aminu Ado Bayero zai angwance nan ba da jimawa da wata tsohuwar zumansa a Kano
  • Majiyoyi sun bayyana cewa, a halin yanzu dai ana ci gaba da shirye-shirye don gwangwaje wannan bikin
  • Majiyoyi sun kara da cewa, ba za a yi wani gagarumin biki ba saboda sarkin baya bukatar biki mai girma

Kano - Sarkin Kano na yanzu, Alhaji Aminu Bayero, na daf da angwancewa da wata tsohuwar zumansa da aka bayyana da suna Hajiyayya da ke zaune a unguwar Dorayi da ke cikin birninsa Kano.

Sarkin wanda ke da mata daya tilo da ‘ya’ya har hudu, zai kara aure ne bayan shekaru talatin da auren matarsa ta farko da yake zaune da ita a ya halin yanzu.

Sarki zai zama ango
Sarkin Kano zai angwance da wata tsohuwar zumansa nan ba da dadewa ba | Hoto: dailynigerian.com
Asali: UGC

Wasu majiyoyi da ke kusa da dangin sun shaidawa jaridar Daily Nigerian cewa ana ci ga da tsare-tsaren bikin a asirce tsakanin wakilan masarautar Kano da kuma danginsu amaryar.

Kara karanta wannan

Nasara: Sojoji sun ragargaji sansanin dan bindiga Bello Turji, sun hallaka da dama

Majiyar ta bayyana cewa baz a ayi wani gagarumin bikin da zai ja hankalin jama'a ba sakamakon sarkin baya bukatar haka.

A cewar majiyar:

“Za a yi daurin auren nan da kwanaki ko makonni. An sha dage shi sau da yawa a baya, kuma tun da zai zama babban taro ba, yana iya faruwa kowane lokaci.
“Sarki ya kasance yana nan Hajiyayye shekaru kafin ya zama sarki. Amma a wannan karon an kammala shirye-shiryen daurin aurensu."

Sarkin dai an haife shi a shekarar 1961, ya kuma hau karagar sarautar Kano a matsayin Sarki na 15 na dangin Fulani a Kano a ranar 9 ga Maris, 2020, bayan tsige dan uwansa Muhammadu Sanusi II da gwamnan jihar, Abdullahi Ganduje ya yi, inji Sahelian Times.

A shekara 90, Sarkin Daura ya auri tsaleliyar Amarya 'yar shekara 20

Kara karanta wannan

Innalillahi: 'Yan bindiga sun sake kai hari Zariya, sun kashe wani mutum, sun sace 'ya'yansa

A wani labarin, Daily Nigerian na ruwaito cewa Mai Martaba Sarkin Daura, Faruk Umar Faruk, ya yi sabuwar Amarya, Aisha Iro Maikano, a ranar Asabar.

An tattaro cewa an yi daurin auren bayan dan gajeren lokaci da Sarkin ya hadu da yarinyar wacce diya ce ga Fagacin Katsina, Iro Maikano.

Hakazalika rahoton ya nuna cewa an daura auren bisa kudin sadaki N1million.

Asali: Legit.ng

Online view pixel