Fadar Shugaban kasa ta jero tulin nasarorin Shugaba Buhari yayin da ya cika shekara 79

Fadar Shugaban kasa ta jero tulin nasarorin Shugaba Buhari yayin da ya cika shekara 79

A ranar Juma’ar nan 17 ga watan Disambn 2021, Muhammadu Buhari ya cika shekara 79 da haihuwa

Shugaba Muhammadu Buhari ya shafe sama da shekara 6 kenan ya na kan karagar mulkin Najeriya

Mai magana da yawun bakinsa, Garba Shehu, ya jero wasu daga cikin nasarorin gwamnatin Buhari

Abuja - Yayin da Muhammadu Buhari ya cika shekara 79 a Duniya, Garba Shehu ya kawo wasu daga cikin nasarori da kalubalen da gwamnatinsa ta samu.

Channels TV tace Malam Garba Shehu ya fitar da jawabi a rabar Alhamis, 16 ga watan Disamba, 2021, inda ya yi bayanin irin kokarin da mai gidansa yake yi.

Mai magana da yawun shugaban Najeriyar yace da gaske gwamnatin tarayya take yi na shawo kan matsalolin da ake fama da su kafin wa’adinta ya kare a 2023.

Annobar COVID-19 ta taba kasashe, amma duk da haka, Garba Shehu yace gwamnatin Muhammadu Buhari tayi kokarin kare mutane da tattalin kasa.

Shin kana da labarin da ka/ki ke son an wallafa ma ka/ki? Ka tuntubemu a info@corp.legit.ng!

Tattalin arzikin kasa

Hadimin shugaban kasar ya bayyana yadda Buhari ya ceto Najeriya daga durkushewar tattalin arziki har sau biyu bayan kasar ta samu kanta a wani irin hali.

Shehu yace a yau tattalin arzikin Najeriya ya mike a sakamakon nasarorin da aka samu a bangaren ICT, noma, da ma’adanai, an rage dogara da arzikin mai.

Shugaba Buhari
Shugaban kasa Buhari Hoto: @GarShehu
Asali: Facebook

Pda ake ciki, asusun kudin kasar wajen Najeriya ya na ta kara tumbatsa, baya ga nasarar da aka samu wajen hana tashin farashin kaya, a cewar Shehu.

Harkar noma da zaman lafiya

Yanzu ana fita da kayan gona da ma’adanai zuwa ketare a dalilin gwamnatin Buhari. Ana samun amfanin gona ne saboda an farfado da kamfanonin taki na gida.

Premium Times tace Garba Shehu ya yi bayanin kokarin da ake yi na kawo zaman lafiya, da neman ganin bayan ‘yan ta’addan da suke hallaka Bayin Allah.

Buhari ya shigo da tsari na musamman da zai sa makiyaya su gujewa kiwon dabbobi a fili, su samu wurin da za su ajiye dabbobinsu, su rika ba su abinci da kansu.

Bayan zuwan Buhari ne aka ci karfin Boko Haram. Sannan an rage karbar cin hanci da rashawa. Wadannan duk su na cikin nasarorin da gwamnatinsa ta samu.

"Wata rana za a manta da duk kalubalen da ake fuskanta a yau. Wannan lokaci zai shiga cikin rubutun da aka yi ruwan gwal a tarihin Najeriya." – Garba Shehu.

Matashin malami ya soki Buhari

An ji cewa malamin jami'a a Kano, Muhsin Ibrahim ya kawo muhawara a shafinsa na Facebook bayan yace shugaba Goodluck Jonathan ya fi Muhammadu Buhari.

Dr. Muhsin Ibrahim ya fadi dalilinsa na cewa tsohon Shugaba Jonathan ya fi Buhari. A cewarsa kuwa wannan ba komai ba ne illa tausayin da Jonathan yake da shi.

Asali: Legit.ng

Online view pixel