Jerin duka 'Yan tawagar Shugaba Buhari yayin da ya bar Najeriya zuwa taro a Turkiyya a yau

Jerin duka 'Yan tawagar Shugaba Buhari yayin da ya bar Najeriya zuwa taro a Turkiyya a yau

  • A yau ne Mai girma Muhammadu Buhari zai bar Najeriya zuwa wani taro da za ayi a kasar Turkiyya
  • Wadanda za su yi wa shugaban kasa rakiya zuwa Istanbul sun hada da uwargidarsa, Hajiya Aisha Buhari
  • Garba Shehu yace abokan tafiyar sun hada da wasu Ministoci, NSA da kuma shugaban hukumar NIA

Abuja - A yau ne shugaban Najeriya, Mai girma Muhammadu Buhari zai tashi ta babban filin jirgin saman Nnamdi Azikiwe da ke babban birnin tarayya.

Jirgin shugaban kasar ba zai tsaya ko ina ba sai birnin Istanbul, inda zai halarci taro da aka shirya domin hadin-kan kasar Turkiyya da kasashen Afrika.

Garba Shehu ya kawo jerin wadanda za su yi wa shugaba Muhammadu Buhari rakiya a wannan tafiya. Jaridar Daily Trust ta fitar da wannan rahoton.

Kara karanta wannan

Da duminsa: Shugaba Buhari da uwargidarsa zasu tafi kasar Turkiyya yau Alhamis

Hadimin yace daga cikin tawagar shugaban kasar akwai mai dakinsa, Aisha Muhammadu Buhari, hadimai da wasu manyan Ministocin tarayya bakwai.

Hadimin da zai bi shugaba Buhari zuwa wannan taro a Turkiyya shi ne mai bada shawara a kan harkar tsaro, Manjo Janar Babagana Monguno (mai ritaya).

Yan tawagar Shugaba Buhari
Buhari da iyalinsa a jirgi Hoto: punchng.com
Asali: UGC

Tawagar ta kuma hada da shugaban hukumar tsaro na NIA, Ambasada Ahmed Rufai Abubakar.

Ministoci 7 za su bi Buhari

Sai Ministoci; Ministan harkokin kasar waje, Geoffrey Onyeama, Ministan kiwon lafiya, Dr. Osagie Ehanire, da Ministan birnin Abuja, Malam Mohammed Bello.

Sai Ministan tsaro, Manjo Janar Bashir Magashi (mai ritaya), Ministan gona, Mohammed Abubakar, da kuma Ministan kasuwanci, Adeniyi Adebayo.

Cikakken jerin tawagar:

1. Aisha Buhari

2. Geoffrey Onyeama

3. Bashir Magashi

4. Mohammed Bello

5. Dr. Osagie Ehanire

Kara karanta wannan

Bayan da SSS suka fatattaki masu zanga-zanga a Katsina, Masari ya kai kara wajen Buhari

6. Mohammed Abubakar

7. Adeniyi Adebayo

8. Babagana Monguno

9. Ahmed Rufai Abubakar.

Asali: Legit.ng

Online view pixel