Ba dan Buhari ba da tuni Najeriya ta zama daular musulunci, inji Lai Mohammed

Ba dan Buhari ba da tuni Najeriya ta zama daular musulunci, inji Lai Mohammed

  • Ministan shugaba Buhari ya bayyana yadda shugaba Buhari ya yi kokari wajen magance matsalolin tsaro
  • Ministan ya ce, ba dan shugaba Buhari ya karbi mulki ba, da yanzu Najeriya ta zama kasar muslunci
  • Ya bayyana haka ne tare da bayyana irin kokarin da shugaba Buhari yayi wajen sanya magance matsalar tsaro a gaba

Abuja - Alhaji Lai Mohammed, ministan yada labarai da al’adu, ya ce ba don ayyukan shugaban kasa Muhammadu Buhari ba, da ‘yan ta’adda sun alanta Najeriya a matsayin daular Musulunci.

Da yake jawabi ga manema labarai a Abuja ranar Laraba, Ministan ya ce ‘yan baya za su tuna alherin Buhari, wanda ya ce ya sanya tsaro ya zama babban abin da gwamnatinsa ta mayar da hankali a kai.

Kara karanta wannan

Shugaba Buhari ba zai iya magance matsalar tsaro a shekara mai zuwa ba, inji minista

Minista Lai Mohammed
Ba dan Buhari ba da tuni Najeriya ta zama daular musulunci, inji Lai Mohammed | Hoto: punchng.com
Asali: UGC

Ya ce a tarihin Najeriya babu wata gwamnati da ta baiwa jami’an tsaro kayan aikin da ake bukata domin magance matsalar rashin tsaro kamar na Buhari, Daily Trust ta ruwaito.

Ya kuma bayyana cewa, tun farkon hawan shugaba Buhari a 2015, shugaban ya mayar da hankali kan kawo hanyoyin magance matsalar tsaro, inda yace hakan ba abin mamaki bane kasancewar yana cikin alkawuran Buhari guda uku.

Punch ta ruwaito Lai Mohammed na cewa:

"Eh, yanayin tsaro ya ci gaba da haifar da babban kalubale, amma a cikin muryoyin da ke cike da rudani - wasu sun damu da halin da ake ciki da gaske wasu kuma suna shirye su yi amfani da shi don son kai - yana da sauki a manta da inda muka fito.

Kara karanta wannan

Labari mai dadi: Shugaba Buhari ya kara wani kaso mai tsoka a albashin 'yan sanda

"A yau, muna duban halin da ake ciki ne kawai, ba tare da tunanin me zai faru ba idan da a ce wannan Shugaban kasa bai yi namijin kokari ba, ta fuskar tsaro.
“Da yadda ‘yan tada kayar baya suke kafin zuwan wannan Gwamnati, tare da iko da wani fili mai fadin da ya kai kasar Belgium, tare da kai hare-hare a baya a kusan jihohi goma sha biyu, ciki har da babban birnin tarayya wanda aka kai wa hari akalla biyar, watakila da sun cimma burinsu na alanta daular Musulunci a Najeriya, in da shugaba Buhari bai taka kara ya karya ba.
“Bayan haka, a 2014, Boko Haram sun alanta Halifanci a Gwoza bayan sun kwace Bama da Gamboru da sauran garuruwa da kauyuka a Borno, Yobe da Adamawa. Sun nada sarakunansu, sun karbi haraji kuma suka daga tutarsu kafin sojoji su tsige su."

Matasan Arewa ga Obasanjo: Kai dai ba ka da bakin sukar gwamnatin shugaba Buhari

Kara karanta wannan

Matasan Arewa ga Obasanjo: Kai dai ba ka da bakin sukar gwamnatin shugaba Buhari

A wani labarin, kungiyar matasan Arewa (NYA) ta ce tsohon shugaban kasa Olusegun Obasanjo ba shi da halin da'a da har zai iya sukar shugaban kasa Muhammadu Buhari.

Obasanjo dai ya bayyana a wani taro a Abuja ranar Litinin, inda ya ce Buhari ya yi iya bakin kokarinsa da zai iya, kuma tsammanin ya kara yin wani abu kamar zaburar da mataccen doki ne.

Sai dai a wata sanarwa da mataimakin sakataren yada labaran NYA na kasa Mohammed Hussani Bauchi ya fitar, ya ce tara mutane domin sukar Buhari ba daidai bane.

Asali: Legit.ng

Online view pixel