Yanzu-Yanzu: 'Yan Bindiga Sun Kutsa Asibiti Sun Sace Likita a Adamawa

Yanzu-Yanzu: 'Yan Bindiga Sun Kutsa Asibiti Sun Sace Likita a Adamawa

  • Wasu miyagun 'yan bindiga sun kutsa asibiti sun sace likita kuma mai asibitin a jihar Adamawa
  • Majiyoyi sun ce yan bindigan sun kai harin ne bayan karfe 6 na yammacin ranar Litinin bayan mutane sun gama sallar magariba
  • Cikin gaggawa suka kutsa cikin asibitin suna harbe-harben bindiga don tarwatsa mutane suka wuce ofishinsa suka yi awon gaba da shi

Jihar Adamawa - 'Yan bindiga sun kutsa wani asibiti a Yola, babban birnin Jihar Adamawa, a ranar Litinin da yamma sun sace mai asibitin, Daily Trust ta ruwaito.

Wanda aka sace din, Dr Saidu Bala, shine tsohon shugaban asibitin kwararru na Yola.

A cewar wata majiya, yan bindigan sun kutsa asibitin ne bayan karfe 6 na yamma, a yayin da mutanen gari ke yin sallar Magariba.

Kara karanta wannan

Babbar Magana: Tsagerun yan bindiga sun kai hari babbar hedkwatar yan sanda ta jiha

Yanzu-Yanzu: 'Yan Bindiga Sun Kutsa Asibiti Sun Sace Likita a Adamawa
'Yan Bindiga Sun Kutsa Asibiti Sun Sace Mai Asibiti a Adamawa. Hoto: The Punch
Asali: UGC

Yadda yan bindigan suka sace likitan

Majiyar ta ce nan take suka fara harbe-harbe bayan sun shiga asibitin, sun rika harbi domin su firgita mutane su tarwatse.

"Yan bindigan sun dira asibitin jim kadan bayan sallar Magariba sannan suka rika harbi a sama don firgita mutane.
"Daga nan sai suka tafi ofishin Dr Saidu Bala suka yi awon gaba da shi. Lamarin ya faru cikin gaggawa ba su kai minti biyar ba ma," a cewar majiyar.

'Yan sanda sun tura jami'ai don ceto likitan

Mai magana da yawun yan sandan jihar Adamawa, DSP Sulaiman Nguroje, ya tabbatar wa Daily Trust da afkuwar lamarin, yana mai cewa an tura jami'ai zuwa yankin domin su ceto likitan su kama masu garkuwar.

Kara karanta wannan

Duk da Jami’an tsaro, ‘Yan bindiga sun dawo titin Kaduna - Abuja, sun yi barin wuta

Ya ce:

"Mutanen sun tsinci kwankwon harsashi guda uku a wurin da aka aikata laifin kuma nan take mun tura jami'ai daga sashin yaki da garkuwa da mutane domin ceto likita da aka sace."

Lamarin ya faru ne a lokacin da ake ta kokawa da karuwar hare-hare a kasar musamman yankin arewa.

'Yan bindiga sun sace babban limami da wasu mutane 10 yayin da suke sallah a Sokoto

A wani labarin, 'yan bindiga sun sace mutane 11 ciki har da babban limami, Aminu Garba, wanda ke shirin jagorantar mutane yin sallah Juma'a a jam'i a kauyen Gatawa da ke karamar hukumar Sabon Birni a Jihar Sokoto.

An sace limamin tare da wasu mutane uku ne a ranar Juma'a kamar yadda Daily Trust ta ruwaito.

Maharan sun tare hanyar Sabon Birnin zuwa Gatawa a ranar Asaba, inda suka bindige mutane uku suka kuma sace wasu mutanen bakwai.

Asali: Legit.ng

Online view pixel