Da Dumi-Dumi: Miyagun yan bindiga sun kai hari hedkwatar yan sanda ta jiha

Da Dumi-Dumi: Miyagun yan bindiga sun kai hari hedkwatar yan sanda ta jiha

  • A kullum matsalar tsaron Najeriya kara yawaita take, yan bindiga na cigaba da cin karen su babu babbaka
  • Wata tawagar miyagun yan bindiga sun kai hari babbar hedkwatar yan sanda ta jihar Abia, amma sun kwashi kashin su a hannu
  • Rahoto ya nuna cewa maharan sun samu nasarar kashe ɗaya daga cikin yan sandan dake bakin aiki

Abia - Wasu tsagerun yan bindiga, ranar Litinin da safe, sun farmaki babbar hedkwatar yan sanda ta jihar Abia dake Umuahia, babban birnin jihar.

Jaridar Vanguard ta ruwaito cewa yan bindigan sun samu nasarar hallaka jami'in ɗan sanda guda ɗaya, wanda ke bakin aiki.

Wata majiya ta shaida wa manema labarai cewa jami'in da suka kashe, wani karamin sufeta, shike aikin gadi a bakin kofar Hedkwatar, wacce ke kan hanyar Bende.

Kara karanta wannan

'Yan bindiga daga Zamfara sun kutsa Filato, sun kai farmaki, sun hallaka mutane 10

Yan sanda
Da Dumi-Dumi: Miyagun yan bindiga sun kai hari hedkwatar yan sanda ta jiha Hoto: placng.org
Asali: UGC

Hakanan kuma majiyar ta kara da cewa maharan sun kai harin ne da misalin ƙarfe 1:00 na daren ranar Lahadi.

Shin kana da labarin da ka/ki ke son an wallafa ma ka/ki? Ka tuntubemu a info@corp.legit.ng!

Mutumin, wanda ke zaune kusa da hedkwatar, ya shaida wa sahara Reporters cewa:

"Da misalin 1:00 na dare, mun ji karar harbe-harbe, da farko mun yi tsammanin yan sanda ne suke harbin domin sukan yi haka don tsorata masu yunkurin kai hari."
"Amma da safe sai muka samu labarin hari ne aka kai musu, kuma maharan sun kashe ɗan sanda ɗaya."

Shin yan sanda sun maida martani?

Rahotanni sun bayyana cewa ɗan sandan da aka kashe shine ya sanar da abokan aikinsa kuma suka tarbe su, inda akai musayar wuta har maharan suka gaza jurewa suka tsere.

Hakanan kuma, an tattaro cewa namijin kokarin da yan sanda masu gadi suka yi, shine yasa maharan ba su kai aikata mummunan nufin da ake tsammanin sun zo da shi ba.

Kara karanta wannan

Karin bayani: Tsagerun yan bindiga sun yi awon gaba da sarakuna biyu, sun ƙone fadarsu da motocinsu

Kakakin rundunar yan sanda reshen jihar Abia, SP Geoffrey Ogbonna, bai ɗaga kiran wayan da aka masa ba, kuma bai turo amsar sakonnin da aka tura masa ba.

Sai dai wani babban jami'i a hukumar yan sandan jihar ya tabbatar da faruwar lamarin, amma ya nemi a sakaya sunansa.

A wani labarin kuma mun kawo muku Abinda Shugaba Buhari ke yi kullum don kawo karshen matsalar tsaro a Najeriya

A kullum shugaba Buhari sai ya yi maganar mutanen da ake kashewa tare da yi musu addu'a, inji fadar shugaban kasa.

Malam Garba Shehu, a wata sanarwa da ya fitar, yace shugaba Buhari yana damuwa fiye da tunani kan halin rashin tsaro da ake ciki.

Asali: Legit.ng

Online view pixel