Duk da Jami’an tsaro, ‘Yan bindiga sun dawo titin Kaduna - Abuja, sun yi barin wuta

Duk da Jami’an tsaro, ‘Yan bindiga sun dawo titin Kaduna - Abuja, sun yi barin wuta

  • Ana zargin ‘yan bindiga sun sake kai hari a hanyar Kaduna zuwa garin Abuja a karshen makon jiya
  • Miyagun ‘yan bindigan sun tsaya kafin a shiga garin Rijana, su na shirin su yi garkuwa da mutane
  • An yi wannan ta’adin ne a daidai lokacin da aka baza sojoji domin su kare rayukan masu bin babban titin

Abuja - Rahotanni sun zo mana cewa miyagun ‘yan bindigan da suka saba tare hanyar zuwa birnin tarayya Abuja, sun sake tare titin a ranar Lahadi.

Sahelian Times ta bayyana cewa wasu ‘yan bindigan sun kai hari a titin na Kaduna zuwa garin Abuja ne da yammacin Lahadi, 12 ga watan Disamba, 2021.

Wadannan mutane sun dawo kan titin, suka buda wuta da nufin su yi garkuwa da matafiya.

Kara karanta wannan

Sheikh Gumi: 'Yan bindiga sun sace yayana, sun kashe dan direban gidanmu

Wani Bawan Allah mai suna Ibrahim Umar da abin ya faru a gaban idanunsa, ya shaidawa manema labarai irin abin da ya gani a ranar Lahadi da yamma.

Ibrahim Umar ya bayyana cewa su na cikin tafiya a cikin motoci, sai suka ji ‘yan bindiga sun buda masu wuta ko ta ina, su na ta harbe-harbe a kan tsakiyar titi.

Titin Kaduna - Abuja
Wata hanya a Abuja Hoto: www.julius-berger.com
Asali: UGC

Shin kana da labarin da ka/ki ke son an wallafa ma ka/ki? Ka tuntubemu a info@corp.legit.ng!

Kamar yadda Umar ya shaidawa ‘yan jarida, wannan abin ya auku ne da kimanin karfe 11:25 na dare.

Har ila yau, wannan mutumi da ya shaida abin da ya faru, ya fadawa manema labarai cewa ‘yan bindigan sun shiga buda masu wuta ne daf da Rijana.

Ana zargin ‘yan bindigan sun yi nasarar hallaka wasu matafiya a cikin wata mota kirar Peugeot J5. Zuwa yanzu babu cikakken labarin abin da ya faru.

Kawo yanzu da muke tattara wannan labari, babu tabbacin adadin mutanen da suka mutu ko suka samu rauni a sakamakon harbe-harben da aka rika yi.

Kara karanta wannan

Matar da tace tana kallo 'yan bindiga suka kona mahaifiyarta da 'ya'ya 4 ta rasu

Miyagun ‘yan bindigan sun sake kafa shigen na su a kan babban titin ne a daidai lokacin da aka baza jami’an sojoji domin su kare masu bin wannan titi.

Ibrahim Umar Bari ya na cikin wadanda aka nemi a tare a wannan hanya da tayi suna wajen satar mutane, ya bayyana abin da ya faru a shafin Facebook.

“Yanzu nan ‘yan bindiga su ka buda mana wuta a babban titin Abuja-Kaduna. Hasbunallahu wa ni'imal wakeel” - Ibrahim Umar Bari

'Dan banga ya zama 'Dan bindiga

Kwanakin baya mu ka ji cewa shugaban JTF da aka kama a Kaduna ya na tare da Miyagun ‘Yan bindiga. Rundunar Sojojin kasa ta fitar da wannan jawabi.

Sunan wannan mutum da aka kama, Aminu Sani. Amma har yanzu ba ayi cikakken bincike domin tabbatar da gaskiya ko rashinsa ga wannan mutum ba.

Asali: Legit.ng

Online view pixel