JAMB ta kirkiro wasu sabbin darusa a manhajar jarrabawar UTME ta shekarar 2022

JAMB ta kirkiro wasu sabbin darusa a manhajar jarrabawar UTME ta shekarar 2022

  • Hukumar jarrabawar shiga jami'a a Najeriya ta JAMB ta bayyana sabbin tsaruka a jarrabawar da ke tafe
  • Hukumar ta bayyana cewa, a halin yanzu za ta kara wasu darrusa biyu na kimiyya a jerin darrusan da ake rubutawa
  • Hukumar ta kuma magantu kan yadda ta shirya sayar ePin a jarrabawar UTME ta shekarar 2022 mai zuwa

Abuja - Hukumar shirya jarabawar shiga makarantun gaba da sakandire ta JAMB ta ce za ta gabatar da sabbin darussan kimiyya guda biyu a jarrabawar JAMB, Punch ta ruwaito.

Magatakardar JAMB, Farfesa Ishaq Oloyede ne ya bayyana haka ranar Asabar 4 ga watan Disamba a Abuja.

Darussan sune Physical Health Education da Computer Science.

Jarrabawar JAMB a Najeriya
JAMB ta kirkiro wasu sabbin darrusa a manhajar jarrabawar shiga jami'a | dateline.ng
Asali: Depositphotos

Oloyede:

Kara karanta wannan

Zan koya wa sauran jam'iyyun siyasa mummunan darasi a 2023, gwamnan Adamawa

"Muna tambaya da wayar da kan jama'a, musamman dalibai, wadanda za su yi jarrabawar, cewa wadannan darussa biyu na kimiyya ne da za a kara a zabinsu don fadada damar da masu rubuta jarrabawa zasu iya samun damar shiga manyan makarantu."

Oloyede ya kuma bayyana cewa nan ba da dadewa ba hukumar za ta kawar da duk wani manakisa na samun damar shiga da manyan makarantun kasar nan ke yi ba bisa ka’ida ba.

Ya ce za a dauki matakin ne domin ganin an dakile shigar da daliban da basu cancanta ba, amma suna da karancin abubuwan da ake bukata.

A baya-bayan nan ne hukumar JAMB ta gano wasu damarmakin shiga na bogi 706,189 daga jami’o’i, da kwalejin kimiyya da fasaha da kwalejojin ilimi da sauran cibiyoyi masu alaka da su.

A cewar shugaban na JAMB:

"Muna so mu ci gaba da gangami don hana masu aikata irin wadannan haramtattun ayyuka su daina yin hakan."

Kara karanta wannan

Wata sabuwa: Gwamnatin Zamfara za ta fara shigo da shanu da awaki daga wasu kasashen waje

Yayin da yake lura da cewa an dauki tsarin rijistar ba tare da tsabar kudi a hannu ba a UTME ta shekarar 2022, Oloyede ya ce JAMB za ta kuma hana cibiyoyin jarabawar kwamfuta sayar da e-PIN don kare kai daga damfarar masu rubuta jarrabawar.

The Nation ta ruwaito batun shi, inda ya kara da cewa:

"An san cewa yawancin cibiyoyin CBT, duk da irin sa idon da ake yi, har yanzu suna amfana da masu rubuta jarrabawa.
“Muna so mu dakatar da hakan; mun tsananta sa ido, amma wani bangare na abin da muke yi shi ne mu tabbatar da cewa mun kare daliban daga wannan karban kudi.
"Za mu tabbatar da cewa duk wanda ke son siyar da ePIN ba zai zama ma'aikacin cibiyar CBT ba. Idan dai kai ma'aikacin cibiyar CBT ne, ka rasa damar siyar da ePIN, domin mu iya daukar masu siyar da ePIN da alhakin abin da suke yi."

Kara karanta wannan

Yanzu-Yanzu: Kotu ta kori karar da ke neman soke takarar gwamna na Soludo a Anambra

Jerin jami'o'i 10 da dalibai suka fi nema a Najeriya, Hukumar JAMB, Ta farko na Arewa

A wani labarin, hukumar shirya jarabawar shiga jami'a, JAMB, ta bayyana cewa jami'ar Ilori da jami'ar Legas, Akoka ne jami'o'i biyu da dalibai sukafi neman shiga a Najeriya.

Wannan na kunshe cikin takardar rahoton hukumar da shugaban hukumar, Farfesa Ishaq Oloyede, ya rattafa hannu, Punch ta samu.

Rahoton ya yi bayanin adadin daliban da suka nemi gurbin shiga kowace jami'a da kuma adadin makin da suka samu.

Asali: Legit.ng

Online view pixel