Wata sabuwa: Gwamnatin Zamfara za ta fara shigo da shanu da awaki daga wasu kasashen waje

Wata sabuwa: Gwamnatin Zamfara za ta fara shigo da shanu da awaki daga wasu kasashen waje

  • Gwamnatin jihar Zamfara ta bayyana kudurinta na shigo da shanu da awaki daga kasashen waje
  • Gwamnatin ta bayyana haka ne yayin wani shirin horas da makiyaya a wasu yankunan jihar ta Zamfara
  • Gwamnati ta bayyana kadan daga cikin manufofinta na kirkirar shirin kawo shanu daga waje don amfanar jihar

Zamfara - Gwamnatin jihar Zamfara ta kammala shirye-shiryen shigo da awaki da shanu daga kasashen Afirka ta Kudu da Norway a wani mataki na bunkasa matsugunan RUGA a jihar, Punch ta ruwaito.

Gwamna Bello Matawalle ne ya sanar da hakan a garin Kaura-namoda yayin taron horas da masu ruwa da tsaki da kuma jajircewa kan ci gaban shirin RUGA da Rahusa Ventures ta shirya wanda Sanata Sahabi Ya’u Kaura ya dauki nauyi.

Kara karanta wannan

Da duminsa: Rayuka 9 sun salwanta a sabon farmakin da miyagun suka kai Plateau

Gwamnan jihar Zamfara, Matawalle
Wata sabuwa: Gwamnatin Zamfara za ta fara shigo da shanu da awaki daga wasu kasashen waje | Hoto: leasdership.ng
Asali: Facebook

Gwamnan wanda ya samu wakilcin kwamishinan gandun daji da kiwo Dr. Ibrahim Abdullahi ya ce za a ajiye dabbobin a RUGA da ke karamar hukumar Maradun domin su zama abin koyi a kokarin gwamnatin jihar na bunkasa matsugunan RUGA.

A cewarsa:

"Tun daga nan mun ba da oda kuma dabbobin za su iso jihar nan ba da jimawa ba,."

Matawalle ya ce an kashe Naira biliyan 2.4 don gina RUGA a karamar hukumar Maradun, inda ya ce an kusa kammala aikin.

Ya jaddada cewa an ware kudi naira biliyan 8.6 domin gina matsugunan RUGA guda uku a shiyyoyin sanatoci uku dake jihar.

Da yake jawabi, baturen taron, Dakta Abdullahi Maiwada, ya ce taron na da nufin horar da masu ruwa da tsaki kan yadda za su raya filayen kiwo na kansu domin gujewa rikici na Fulani makiyaya.

Kara karanta wannan

Jami'an kwastam sun kwace tirela 12 ta shinkafa da miyagun kwayoyi a Ogun

Ya ce:

“An zabo mahalarta 250 daga kananan hukumomi uku na shiyyar Sanatan Zamfara ta Arewa wadanda akasari manoma, makiyaya, shugabannin gargajiya da na siyasa ne”.

Maiwada ya ce yayin da masu ruwa da tsaki za su iya shirya wuraren kiwo nasu, za a rage rikicin Fulani makiyaya da ‘yan bindiga da satar shanu ko kuma kawar da su gaba daya.

Ya yabawa Sanata Sahabi Yau bisa shirya taron bitar a matsayin wani bangare na ayyukan mazabar sa, inda ya yi kira ga daukacin ‘yan siyasar jihar da su yi koyi da shi, kamar yadda Street Journal ta ruwaito.

Babbar magana: 'Yan bindiga sun kai wa 'yan sanda wasikar sanarwar kai hari a Zamfara

A wani labarin, rundunar ‘yan sandan jihar Zamfara ta tabbatar da cewa ta samu wasikar barazanar kai hari a wani coci-coci a Gusau, babban birnin jihar.

Kwamishinan ‘yan sandan jihar, Ayuba Elkanah, ya ce wasu da ba a san ko su wanene ba ne suka jefar da wasikar a hedikwatar ‘yan sandan jihar.

Kara karanta wannan

N2.3tr muka ware don rabawa yan Najeriya kayan tallafin Korona, Gwamnatin tarayya

Ya bayyana hakan ne a wata tattaunawa da manema labarai a Gusau ranar Talata, SaharaReporters ta ruwaito.

Asali: Legit.ng

Online view pixel