Jerin jami'o'i 10 da dalibai suka fi nema a Najeriya, Hukumar JAMB, Ta farko na Arewa
- Hukumar JAMB ta saki lambar adadin daliban da suka nemi shiga jami'a bana
- Manyan jami'o'in Arewa daga Arewa na cikin jami'o'i goma da aka fi nema
- Jami'ar Ilori dake jihar Kwara, Arewa maso tsakiyar Najeriya ce ta farko
Abuja - Hukumar shirya jarabawar shiga jami'a, JAMB, ta bayyana cewa jami'ar Ilori da jami'ar Legas, Akoka ne jami'o'i biyu da dalibai sukafi neman shiga a Najeriya.
Wannan na kunshe cikin takardar rahoton hukumar da shugaban hukumar, Farfesa Ishaq Oloyede, ya rattafa hannu, Punch ta samu.
Rahoton ya yi bayanin adadin daliban da suka nemi gurbin shiga kowace jami'a da kuma adadin makin da suka samu.
Rahoton yace a jarabawar 2021 da aka zana, mutum 1,312,992 ne suka zauna jarabawar UTME. Yayinda mutum 168,613 suka samu maki 200 da abinda yayi sama; mutum 236,936 kuma ci 190-200.
Hakazalika mutum 327,624 sun samu 180 zuwa 190, kuma mutum 445,597 sun ci 170 - 179.
Shin kana da labarin da ka/ki ke son an wallafa ma ka/ki? Ka tuntubemu a info@corp.legit.ng!
Ga jerin jami'o'in 10 da dalibai suka fi nema da adadin mutanen da suka nema:
1. Jami'ar Ilori (UNILORIN) - 78,466
2. Jami'ar Legas (UNILAG) - 59,190,
3. Jami'ar Benin, (UNIBEN) - 49,763;
4. Jami'ar Najeriya (UNN) - 47,239;
5. Federal University, Oye-Ekiti, 45,920;
6. Jami'ar Ahmadu Bello Zaria (ABU) - 44,509;
7. Jami'ar Bayeri Kano (BUK) 44,352;
8. Jami'ar Nnamdi Azikiwe - 43542;
9 Jami'ar Obafemi Awolowo - 42, 614
10. Jami'ar Jos (UNIJOS) - 38,309.
Yajin-aiki: A zargi Gwamnatin Najeriya idan muka dauki mataki na gaba inji Kungiyar ASUU
Kungiyar malaman jami’a na kasa, ASUU, ta fara maganar kiran taron gaggawa na majalisar koli ta NEC a makon nan, domin tayi zama.
Jaridar The Nation ta ce hakan ya zama dole ne bayan wa’adin da kungiyar ta ASUU ta ba gwamnatin tarayya ya cika a karshen watan Agusta.
Bayan wannan zama, ASUU tace za ta tattauna da duk masu fada-a-ji a duka rassan kungiyar, idan dai gwamnati ta gaza cika alkawuran da ta dauka.
Asali: Legit.ng