'Yan sanda sun damke 'yan bindiga 2 a Neja, sun kwato shanu 71 da tumaki 23 a hannunsu

'Yan sanda sun damke 'yan bindiga 2 a Neja, sun kwato shanu 71 da tumaki 23 a hannunsu

  • ‘Yan sanda a jihar Neja sun kama wasu mutane 2 da ake zargin ‘yan bindiga ne, sannan sun amshe shanu 71 da tumaki 23 da ake zargin sun sato
  • Jami’in hulda da jama’an rundunar, DSP Wasiu Abiodun, ya bayyana hakan a wata takarda ta ranar Juma’a a Minna
  • A cewarsa lamarin ya auku ne da misalin 6pm na ranar 30 ga watan Satumba, kuma jami’an ofishin Gawu-Babangida ne su ka samu nasarar kama su

Neja - Rundunar ‘yan sandan jihar Neja sun samu nasarar kama wasu mutane biyu da ake zargin ‘yan bindiga ne sannan an amso shanu 71 da tumaki 23 da ake zargin sun sato, NewsWireNGR ta ruwaito.

Jami’in hulda da jama’an rundunar, DSP Wasiu Abiodun, ya bayyana hakan a wata takarda ta ranar Juma’a a Minna.

'Yan sanda sun damke 'yan bindiga 2 a Neja, sun kwato shanu 71
An kama 'yan bindiga 2 a Neja, an kwato shanu 71 a hannunsu: Hoto: Channels TV
Asali: UGC

A cewarsa a ranar 30 ga watan Satumba da misalin karfe 6pm, jami’an ofishin Gawu-Babangida sun kama maza biyu bayan samun wasu bayanai.

Ana zargin sato shanun su ka yi a wata kasuwar shanu

Kamar yadda ya shaida:

“An ga wadanda ake zargin a kasuwar shanun Izom da tumaki biyu da ake zargin sun sato.
“Ana zargin sun sato su ne daga kauyen Zazagha da ke karamar hukumar Munya a jihar, a ranar 26 ga watan Nuwamba.”

Kakakin rundunar a yadda NewsWireNGR ta ruwaito, ya ce mutanen yankin ne su ka fara kai wa ‘yan sandan rahoto.

Yayin da aka tasa su da tambayoyi, wadanda ake zargin sun tabbatar da cewa su na cikin kungiyar ‘yan bindiga goma da su ka kai farmaki Kauyen Chibani da Dnalakpe ta Zazagha sannan su ka sace shanu.

Bayan an titsiye su, an amso shanu 71 da tumaki 23 daga hannunsu yayim da su ke tafiya shanun daga dajin Zazagha wuraren Kwali da ke Abuja.

Yanzu haka ‘yan sanda na kokaron nemo sauran abokan harkarsu

Abiodun ya ce yanzu haka ‘yan sanda su na kokarin kama sauran ‘yan bindigan.

A cewarsa kwamishinan ‘yan sandan jihar, Mr Monday Kuryas, ya tabbatar wa da mazauna yankin cewa a tsaye suke wurin tabbatar da an kawar da duk wani ta’addanci a jihar.

Kuryas ya bukaci mazauna yankin da su dinga bayar da bayanai masu amfani ga ‘yan sanda da sauran jami’an tsaron da ke jihar don kawo karshen ta’addanci.

Hotunan Mutane 5 Masu Garkuwa Da Mutane Da Ƙwararrun Mafarauta Suka Kama a Kogi

A wani labarin daban, kwararrun mafarauta a karamar hukumar Okehi a jihar Kogi sun yi nasarar kama mutane biyar 'yan kungiyar masu garkuwa da mutane, LIB ta ruwaito.

An kama mutane biyar din da ake zargi a safiyar ranar Talata a Atami, wani gari da ke wajen Osara a ranar Talata, 27 ga watan Satumban shekarar 2021.

King Habib, babban hadimi ga shugaban karamar hukumar Okehi a bangaren watsa labarai, Hon Abdulraheem Ohiare Ozovehe ya tabbatar da kama wadanda ake zargin, yana mai cewa tawagar sun dade suna adabar mutane a titin Okene-Lokoja da Okene-Auchi a jihar Kogi State.

Asali: Legit.ng

Online view pixel