Na janyo wa jama'ar Yesu abin kunya: Faston da aka kama ya yi garkuwa da Faston Katolika

Na janyo wa jama'ar Yesu abin kunya: Faston da aka kama ya yi garkuwa da Faston Katolika

  • Jami’an rundunar ‘yan sandan jihar Imo sun kama wani Fasto Izuchukwu Anoloba mai shekaru 35 bisa zarginsa da garkuwa da wani faston na cocin katolika, Fidelis Ekemgba
  • Yayin da aka ake holen wanda ake zargin tare da wasu masu laifin, Kwamishinan rundunar, Rabiu Hussaini ya ce wanda ake zargin ya rike limamin na fiye da kwana bakwai
  • Bayan haka sun bukaci a biya N5,000,000 kafin su sake shi, daga nan jami’an binciken sirri su ka yi gaggawar bankado su a jihar Legas sannan su ka yi ram da shi

Jihar Imo - Jami'an 'yan sanda a jihar Imo sun kama wani fasto Izuchukwu Anoloba, mai shekara 35, da wasu kan garkuwa da babban Faston Katolika, Fidelis Ekemgba, The Punch ta ruwaito.

Kara karanta wannan

An kama mai faskare saboda fizgar mazakutar mai gidansa da rashin jituwa ya shiga tsakaninsu

Da ya ke holen wadanda ake zargin da wasu, kwamishinan yan sandan jihar, Rabiu Hussaini, ya ce wadanda ake zargin sun tsare babban faston tsawon kwana bakwai suka karbi kudin fansa Naira miliyan 5.

An kama Faston da ya yi garkuwa da babban Faston Katolika, ya roƙi Allah ya yi masa gafara
Fasto ya yi garkuwa da babban faston katolika. Hoto: The Punch
Asali: Facebook

Kwamishinan ya nuna farincikinsa akan kamen da yaransa su ka yi

Kwamishinan ya bayyana yadda aka kama faston a Legas bayan jami’an binciken sirri sun gano inda suke.

A cewarsa faston katolikan ne mai kula da cocin St Peters Parish da ke Umunohu Amakaohia da ke karamar hukumar Ihitte/Uboma a jihar.

Kuma wadanda su ka yi garkuwa da shi sunci amanarsa ne kafin su sace shi.

Jaridar The Punch ta ruwaito yadda ya kara da yaba wa yaransa akan aikin kwarai da suka yi inda kwamishinan ya ce za a ci gaba da yin hakan don kawo gyara ga tsaron jihar.

Kara karanta wannan

Da Duminsa: 'Yan bindiga sun bude wa motar kwamishina wuta a Kogi

Faston ya ce ya samu N1,500,000 a matsayin kasonsa

Yayin tattaunawa da manema labarai, Aboloba ya ce ya samu naira miliyan daya da rabi ne daga cikin kudaden da aka amsa na fansar faston katolikan.

Kamar yadda ya shaida:

“Ni faston Apostolic Church of Christ da ke jihar Legas ne. Kuma na samu naira miliyan daya da rabi ne a matsayin kaso na. Ban taba sanin za a iya gano ni ba. Na yi danasani don yanzu na janyo wa jama’an yesu da iyalaina abin kunya.”

Kotu ta ɗaure wani matashi da ya yi asubanci ya tafi coci ya sace kujerun roba

A wani rahoton, wata kotun majistare ta daure wani matashi, Lekan Alaka, mai shekaru 19, watanni 3 bisa satar kujerun roba masu kimar N91,200 daga cocin Mount Zion Angelican.

‘Yan sandan sun kama Alaka da laifin sata kamar yadda Vanguard ta ruwaito.

Kara karanta wannan

Zamfara: An kama wata mata da harsashi 991 na AK-47 za ta kai wa hatsabibin shugaban ƴan ta'adda

Alkali Olajumoke Somefun ya yanke hukunci bisa tabbatar da laifin da ya aikata bisa ruwayar Vanguard.

Asali: Legit.ng

Online view pixel