Hotunan Mutane 5 Masu Garkuwa Da Mutane Da Ƙwararrun Mafarauta Suka Kama a Kogi
- Mafarauta sun yi nasarar kama wasu maza biyar da ake zargi masu garkuwa ne a jihar Kogi
- Wadanda aka kama din sun hada da Tukur Saleh, Ahmadu Sanni, Yusuf Sanni daga Bauchi sai Abubakar Saleh (Baba Wuro) da Isah Saleh daga jihar Kano
- Hon Abdulraheem Ohiare Ozovehe, shugaban karamar hukumar ya tabbatar da kama bata garin ya kuma ce an mika su hannun jami'an tsaro
Jihar Kogi - Kwararrun mafarauta a karamar hukumar Okehi a jihar Kogi sun yi nasarar kama mutane biyar 'yan kungiyar masu garkuwa da mutane, LIB ta ruwaito.
An kama mutane biyar din da ake zargi a safiyar ranar Talata a Atami, wani gari da ke wajen Osara a ranar Talata, 27 ga watan Satumban shekarar 2021.
Shin kana da labarin da ka/ki ke son an wallafa ma ka/ki? Ka tuntubemu a info@corp.legit.ng!
King Habib, babban hadimi ga shugaban karamar hukumar Okehi a bangaren watsa labarai, Hon Abdulraheem Ohiare Ozovehe ya tabbatar da kama wadanda ake zargin, yana mai cewa tawagar sun dade suna adabar mutane a titin Okene-Lokoja da Okene-Auchi a jihar Kogi State.
Sanarwar ta ce a halin yanzu an mika wadanda ake zargin a hannun jami'an tsaro yayin da ake cigaba da zurfafa bincike domin kwato muggan makamai da suke da shi, rahoton LIB.
Wadanda aka kama din sun ne: Tukur Saleh, Ahmadu Sanni, Yusuf Sanni, dukkansu daga Bauchi; Abubakar Saleh (Baba Wuro) da Isah Saleh, su kuma daga jihar Kano.
Hon Ohiare ya ce:
"Ba za mu yi kasa a gwiwa ba wurin ganin mun kawar da bata gari daga karamar hukumar Okehi da kewaye."
Sarkin Katsina ya barranta da matsayar Sheikh Gumi: Kisa ya dace da ƴan bindiga ba tattaunawa da su ba
A wani labarin daba, mai martaba Sarkin Katsina ya ce tunda ƴan bindiga sun zaɓi su rika kashe mutane 'suma bai dace a bar su da rai ba'.
Sarkin na Katsina, Abdulmuminu Usman ya ce ba abin da ya dace da ƴan bindigan da ke kashe mutane a arewa maso yamma illa kisa.
Sarkin ya yi wannan furucin ne yayin taron tsaro na masu ruwa da tsaki a ranar Talata a Katsina kamar yadda Premium Times ta ruwaito.
Asali: Legit.ng