Jami'an kwastam sun kwace tirela 12 ta shinkafa da miyagun kwayoyi a Ogun

Jami'an kwastam sun kwace tirela 12 ta shinkafa da miyagun kwayoyi a Ogun

  • Hukumar kwastam ta kasa reshen jihar Ogun, ta kama buhunan shinkafar gwamnati 7,311 dankare a tirela 12 a jihar
  • Shugaban hukumar na reshen jihar, Dera Nnadi, ya ce jami'ai sun kama fakiti 124 da sunki 164 na wiwi mai nauyin 167kg
  • Nnadi ya sanar da cewa sun kama motoci ashirin a jihar tare da babura biyu wadanda ake amfani da su wurin shigo da haramtattun kaya

Ogun - Jami'an hukumar kwastam ta kasa, reshen jihar Ogun ta kama buhu 7,311 na shinkafar gwamnati wacce aka loda a tireloli 12 a jihar.

Har ila yau, ta kama fakiti 124 da sunki 164 na wiwi mai nauyin 167kg, Punch ta ruwaito.

Shugaban hukumar na yankin, Dera Nnadi, ya bayyana hakan a ranar Laraba yayin zantawa da manema labarai a ofishin NCS da ke Abeokuta, babban birnin jihar.

Read also

Kungiyar musulmai a Arewa ta tsakiya: A tsayar da dan yankin shugabancin kasa a zauna lafiya

Jami'an kwastam sun kwace tirela 12 ta shinkafa da miyagun kwayoyi a Ogun
Jami'an kwastam sun kwace tirela 12 ta shinkafa da miyagun kwayoyi a Ogun. Hoto daga punchng.com
Source: UGC

Shugaban ya bayyana cewa, hukumar ta cafke wasu mutum biyu wadanda ke kokarin kai kwayoyi Ijebu-Ode da ke kan hanyar kudu maso gabas.

Shugaban ya ce an kama wasu miyagun kwayoyin a yankunan da ke kusa da iyaka a jihar. Nnadi ya ce hukumar ta kwace lita dari uku na man girki, dila hudu ta gwanjo, buhuna ashirin da shida na takalma da kuma buhu hudu na kayan wasan yara.

Kamar yadda yace, sauran kayayyakin da aka kwace sun hada da bandir biyu da wasu hudu na tayoyi da takardu, kwalaye 810 na kaji, lita 20,775 na fetur a jarkuna 831 da sauransu.

Kamar yadda Punch ta ruwaito, hukumar kwastam din ta kasa ta kwace ababen hawa ashirin da babura biyu wadanda ake amfani da su wurin kwasar kayan da aka hana shigowa da su.

Read also

Yanzu-Yanzu: EFCC ta sanya gwamnan Anambra a jerin sunayen wadanda take nema

"A sani cewa, umarnin gwamnatin tarayya kan rufe iyaka har yanzu ta na nan. Don haka babu kudin shiga da ake samu daga shigo da kayayyaki," ya kara da cewa.

Nnadi ya ja kunnen 'yan sumogal da ke jihar kan su kiyaye yin zagon kasa ga tattalin arzikin kasa.

Jama'a na neman mafaka bayan jami'an kwastam sun bude musu wuta kan kisan abokin aikinsu

A wani labari na daban, jami'an hukumar kwastam ta kasa, NCS, sun fada wani kauye da ake kira Fagbohun da ke karamar hukumar Yewa ta jihar Ogun inda suka gigita kauyen.

An zargi fusatattun jami'an kwastam din da banka wa wasu gidaje, babura tare da kakkabe fadar dagacin kauyen kuma suka cafke wasu jama'a, Daily Trust ta wallafa.

Wannan ya biyo bayan kisan gillar da aka yi wa jami'an kwastam biyu bayan arangamar da suka yi da 'yan sumogal a makon da ya gabata.

Read also

Hukumar kwastam ta yi ram da tulin Tramadol a filin jirgin saman dakon kaya

Source: Legit

Online view pixel