Da duminsa: Rayuka 9 sun salwanta a sabon farmakin da miyagu suka kai Plateau

Da duminsa: Rayuka 9 sun salwanta a sabon farmakin da miyagu suka kai Plateau

  • Rayuka a kalla tara ne suka salwanta a kauyen Te'egbe da ke karamar hukumar Bassa ta jihar Filato sakamakon kutsen 'yan bindiga
  • A sabon farmakin da miyagun suka kai wurin karfe 1 na daren Juma'a, mutane da yawa sun jigata kuma gidaje masu yawa duk sun kone
  • Gwamna Lalong ya yi Allah wadai da aukuwar lamarin inda ya tabbatar da cewa za a tallafawa wadanda lamarin ya shafa kuma a zakulo miyagun

Filato - A kalla rayuka tara ne suka halaka yayin da wasu na daban suka jigata sakamakon farmakin da 'yan bindiga suka kai kauyen Te'egbe a karamar hukumar Bassa ta jihar Filato.

Daily Trust ta ruwaito cewa, gidaje masu tarin yawa duk sun babbake.

Da duminsa: Rayuka 9 sun salwanta a sabon farmakin da miyagun suka kai Plateau
Da duminsa: Rayuka 9 sun salwanta a sabon farmakin da miyagun suka kai Plateau. Hoto daga dailytrust.com
Asali: UGC

An kai farmakin kauyen ne bayan kwana biyu da aka yi wa wasu manoma kwanton bauna kuma aka kashe su a kauyen Miango da ke masarautar Irigwe a karamar hukumar Bassa ta jihar.

Kara karanta wannan

Hanyoyi 5 da za'a ka iya kare ban dakin zamani daga macizai

Davidson, mai magana da yawun kungiyar cigaban Irigwe, wanda ya tabbatar da aukuwar lamarin ga Daily Trust, ya ce wadanda suka kai farmakin sun kutsa kauyen ne wurin karfe 1 na daren Juma'a.

Shin kana da labarin da ka/ki ke son an wallafa ma ka/ki? Ka tuntubemu a info@corp.legit.ng!

Gwamna Simon Bako Lalong na jihar a wata takarda da ya fitar ta hannun daraktan yada labarai da hulda da jama'a nashi, Dr Makut Simon Machan, ya kushe wannan farmakin inda yayi kira ga hukumomin tsaro da su zakulo miyagun.

Lalong, yayin jajanta wa wadanda lamarin ya shafa da iyalansu, ya tabbatar da cewa gwamnati za ta yi adalci kuma sai ta bankado wadanda suka aikata wannan barnar.

Lalong ya kara da umartar hukumar kai agajin gaggawa ta jihar Filato da su gaggauta kai ziyara yankin kuma su duba yanayin barnar da aka yi tare da kai wa jama'ar wurin kayan rage radadi.

Kara karanta wannan

Rahoto: 'Yan Zamfara sun shiga damuwa, 'yan bindiga sun fara karbar harajin noma

Ya kara da kira ga jama'a da su taimaki jami'an tsaro da bayanan da ya dace wadanda za su basu damar gano miyagun da ke barna tare da dalilinsu na addabar jama'a.

Kisan Musulmai a Jos: Majalisar malamai ta ce kada Musulmai su dauki doka a hannu

A wani labari na daban, majalisar Malamai/Dattawa ta Jihar Filato ta yi kira ga al’ummar Musulmi da ke Jos da kada su kai farmaki kan kowa don daukar fansa kan kisan da aka yi wa musulmai a kan hanyar Gada-biyu - Rukuba, cikin Karamar Hukumar Jos ta Jihar Filato.

An kashe wasu Fulani matafiya musulmai a ranar Asabar a kan hanyarsu ta komawa jihohin Ondo da Ekiti bayan sun halarci wani hidiman addini a Bauchi, an kai musu hari inda aka kashe sama da 20, mutane da yawa sun ji rauni kuma kusan 10 sun bace.

Kara karanta wannan

‘Yan bindiga sun sake kai hari Filato, sun kashe mutane biyu

A rahoton Daily Trust, ta ce wata sanarwa mai dauke da sa hannun babban sakataren kungiyar, Ahmad Muhammad Ashir ya ce:

"Musulunci bai goyon bayan tashin hankali saboda haka bai kamata a kai hari ko kashe wani da sunan daukar fansa ba."

Asali: Legit.ng

Online view pixel