N2.3tr muka kashe wajen rabawa yan Najeriya kayan tallafin Korona, Gwamnatin tarayya

N2.3tr muka kashe wajen rabawa yan Najeriya kayan tallafin Korona, Gwamnatin tarayya

  • Babban jami'in Gwamnatin Najeriya ya bayyana adadin kudin da aka ware don tallafin annobar Korona
  • Gwamnati ta fito da tsare-tsare daban-daban a shekarar 2020 domin rage radadin annobar Korona kan yan Najerya
  • Yanzu kuma gwamnatin na kashe makudan kudade don samawa yan Najeriya rigakafin cutar

Uyo - Karamin Ministan Kasafin Kudi, Prince Clem Agba, ya bayyana cewa gwamnatin tarayya ta kashe sama da N2.3trillion wajen kayan tallafin rage radadin cutar Korona a 2020.

Agba ya bayyana hakan ranar Talata a taron wakho da ofishin Akawunta Janar na tarayya ya shirya a Uyo, birnin jihar Akwa Ibom, rahoton Punch.

A cewarsa, kudaden sun hada da tallafin da aka baiwa jihohi, yan kasuwa, iyalai da daidaikun mutane ta hanyar kyautar kudi da yafe haraji.

Kara karanta wannan

Nan da watanni uku ku kara kudin man fetur: Bankin duniya ga Gwamnatin Najeriya

Ya ce:

"COVID-19 da ta fara mamaye duniya matsayin annobar kiwon lafiya ta zama annobar tattalin arziki, amma saboda saurin farfado da tattalin arzikin, mun samar da hanyoyi wanda suka hada da; tallafin kudi, da neman taimako daga kasashen waje."
"Mun yi hakan ne domin samar da ayyukan yi da kuma takaita rasa ayyukan da mutane keyi."
"Zamu cigaba da fadada hanyoyin rage radadin da kudi N2.3tr da Gwamnatin tarayya ta ware."

Gwamnatin tarayya
N2.3tr muka kashe wajen rabawa yan Najeriya kayan tallafin Korona, Gwamnatin tarayya Hoto: Clement Agba
Asali: Facebook

Shirin kara farashin mai: N200bn zamu rika kashewa a wata wajen rabawa yan Najeriya N5000

A wani labarin kuwa, Gwamnatin tarayya ta ce za ta rika kashe N200 billion a wata wajen rabawa talakawan Najeriya kudi domin rage zafin da cire tallafin mai zai haifar.

Idan Gwamnati ta cire wannan tallafi, kudin man fetur zai yi tashin gwauron zabo.

Kara karanta wannan

Shirin karin farashin mai: N200bn zamu rika kashewa a wata wajen rabawa yan Najeriya N5000

Leadership newspaper ta ruwaito cewa Ministar Kudi, Zainab Ahmed, ta bayyana hakan ne ranar Talata, 23 ga Nuwamba 2023 a taron kaddamar da rahoton Bankin Duniya (NDU).

A cewarta, talakawan dake Najeriya mutum guda milyan 30 zuwa 40 za'a rika baiwa wannan kudi wata-wata.

Tace amma sai an cire tallafin za'a san adadin yan Najeriya da zasu samu wannan kudi.

Asali: Legit.ng

Online view pixel