Wadanda suka tsere daga gidan yarin Kogi ne ke da alhakin kai hari Masallacin Neja, 'Yan sanda

Wadanda suka tsere daga gidan yarin Kogi ne ke da alhakin kai hari Masallacin Neja, 'Yan sanda

  • Kakakin rundunar 'yan sandan Najeriya ya ce sun cafke miyagun da suka kai wa masallata farmaki a jihar Neja
  • Kamar yadda ya bayyana, an gano maharan suna daga cikin masu laifi da suka tsero daga gidan gyaran halin jihar Kogi
  • Fanka Mba ya tabbatar da kamen miyagun da ke kaiwa matafiya farmaki a kan titin Kaduna zuwa Abuja

Mai magana da yawun rundunar 'yan sandan Najeriya, Frank Mba, ya ce an cafke wadanda ake zargi har 32 kan hannunsu a laifuka daban-daban da suka hada da garkuwa da mutane, sumogal din makamai da satar motoci.

A wata takarda da ya fitar a ranar Talata, Mba ya ce jami'an runduna ta musamman sun damke wadanda ake zargi daga wurare daban-daban na yankin arewa ta tsakiya, arewa ta yamma, arewa maso gabas da sauran yankuna, TheCable ta ruwaito.

Kara karanta wannan

Yan bindiga da Sojojin sun yi musayar wuta a Imo kan umarnin zama a gida na IPOB

Wadanda suka tsere daga gidan yarin Kogi ne ke da alhakin kai hari Masallacin Neja, 'Yan sanda
Wadanda suka tsere daga gidan yarin Kogi ne ke da alhakin kai hari Masallacin Neja, 'Yan sanda. Hoto daga thecable.ng
Asali: UGC

Kamar yadda yace, wasu daga cikin wadanda ake zargin suna da hannu a cikin farmakin da aka kai wa masallata a jihar Neja. Su ne ake zargin sun tsere daga gidan gyaran halin da ke Lokoja a jihar Kogi.

A cikin watan Satumba, 'yan bindigan sun balle gidan gyaran halin jihar Kogi inda daruruwan wadanda ke tsare suka tsere, TheCable ta ruwaito.

Mai magana da yawun rundunar 'yan sandan ya ce wadanda aka kama har da masu kai wa matafiya kan babbar hanyar kaduna zuwa Abuja farmaki inda ya kara da cewa an ceci wasu mutane ba tare da sun jigata ba.

Sabon hari: 'Yan bindiga sun kai hari masallaci, sun bindige masallata a jihar Neja

A wani labari na daban, Daily Nigerian ta ruwaito cewa, wasu ‘yan bindiga sun kai hari a wani masallaci a kauyen Maza-Kuka da ke karamar hukumar Mashegu ta jihar Neja, inda suka kashe wasu masallata 18.

Kara karanta wannan

Rundunar 'yan sanda ta sanar da yadda miyagu suka yi garkuwa da DPO a Edo

An tattaro cewa, ‘yan bindigar sun mamaye kauyen ne da yawan gaske inda suka far wa mutanen kauyen da ke gudanar da sallar asuba.

Sakataren gwamnatin jihar Neja Ahmed Ibrahim-Matane ya tabbatar wa jaridar The Nation faruwar harin. Ya ce an kashe mutane 16 a masallacin nan take yayin da aka kashe daya a kauyen Kaboji a wani harin na daban.

Asali: Legit.ng

Online view pixel