Rundunar 'yan sanda ta sanar da yadda miyagu suka yi garkuwa da DPO a Edo

Rundunar 'yan sanda ta sanar da yadda miyagu suka yi garkuwa da DPO a Edo

  • Kakakin rundunar 'yan sandan jihar Edo ya tabbatar da garkuwa da DPO na ofishin Fugar da miyagu suka yi a jihar
  • Ya sanar da cewa miyagun sun bayyana daga daji inda suka bude wa motar DPO wuta yayin da ya ke tare da dogarinsa
  • Dole ta sa suka tsaya inda aka tasa su zuwa daji amma dogarin DPO, sajan Aliu ya samu nasarar tserewa

Edo - Rundunar 'yan sandan jihar Edo ta tabbatar da garkuwa da DPO, CSP Ibrahim Ishaq na ofishin yankin Fugar da ke karamar hukumar Etsako ta jihar da miyagun 'yan bindiga suka yi.

A wata takarda, kakakin rundunar, Bello Kongtons, ya ce kwamishinan 'yan sandan jihar, Philip Ogbadu, ya ce an sace DPO a ranar 26 ga watan Nuwamban 2021.

Rundunar 'yan sanda ta sanar da yadda aka yi garkuwa da DPO a Edo
Rundunar 'yan sanda ta sanar da yadda aka yi garkuwa da DPO a Edo. Hoto daga dailytrust.com
Asali: UGC
"DPO na kan hanyarsa ta zuwa Aghenebode a motarsa tare da dogarinsa Sajan Aliyu kuma duk suna sanye da farin kaya ne yayin da miyagun suka tsare su a wurin Ekwuosor," takardar tace.

Kara karanta wannan

Kano: 'Yan kasuwa sun koka kan jagoranci rushe shaguna da shugaban KAROTA yayi a kasuwar waya

Ya ce kwatsam 'yan bindigan suka bayyana daga daji kuma suka bude wa motar wuta, lamarin da yasa dole suka tsaya, Daily Trust ta ruwaito.

Shin kana da labarin da ka/ki ke son an wallafa ma ka/ki? Ka tuntubemu a info@corp.legit.ng!

Kamar yadda yace, sun tasa keyar 'yan sandan zuwa daji yayin da dogarin DPO ya tsere.

Kwamishinan 'yan sandan jihar ya yi kira ga jama'a da su kwantar da hankulansu kuma su cigaba da al'amuransu saboda rundunar na kokarin shawo kan matsalar.

Daily Trust ta tattaro cewa, masu garkuwa da mutanen sun bukaci kudin fansa har N50 miliyan amma kakakin rundunar 'yan sandan ya yi shiru kan hakan.

Nasarawa: 'Yan sanda sun bankado yunkurin sace jigon PDP

A wani labari na daban, Rundunar 'yan sandan jihar Nasarawa ta bankado yunkurin sace wani Umar Nasiru-Black, shugaban jam'iyyar Peoples Democratic Party (PDP) na yankin Nasarawa ta kudu.

Kara karanta wannan

'Yan sanda sun yi ram da dan fashin da yayi basaja kamar makiyayi

Daily Trust ta ruwaito cewa, kakakin rundunar 'yan sandan jihar, Ramhan Nanseli, ya bayyana hakan a wata takarda da ya fitar a ranar Lahadi a garin Lafia.

Ya ce, "A ranar Asabar, 20 ga watan Nuwamba wurin karfe takwas na dare, mun samu kira kan cewa 'yan bindiga shida sun kutsa gidan shugaban PDP wanda ke yankin Bukan Kwato da ke Lafia kuma sun yi yunkurin garkuwa da shi.
"Bayan samun wannan bayani, kwamishinan 'yan sandan jihar, Adesina Soyemi, ya gaggauta aika kungiyar sintiri ta 'yan sanda da ke yankin zuwa gidan tare da bankado kokarin garkuwa da shi."

Asali: Legit.ng

Online view pixel