Yan bindiga da Sojoji sun yi musayar wuta a Imo kan umarnin zama a gida na IPOB

Yan bindiga da Sojoji sun yi musayar wuta a Imo kan umarnin zama a gida na IPOB

  • Dakarun sojin Najeriya da wasu 'yan bindiga sun yi musayar wuta a jihar Imo da sanyin safiyar yau Talata
  • Rahotanni sun bayyana cewa, 'yan bindigan na kokarin tabbatar da umarnin zama a gida na IPOB ne lokacin da suka yi karo
  • Har zuwa lokacin hada wannan rahoton, babu labarin adadin raunuka ko asarar rayuka a yayin fafatawar

Imo - Dakarun sojin Najeriya da wasu ‘yan bindiga sun yi kazamin musayar wuta a Mgbidi da Akata da ke karamar hukumar Oru ta Yamma a jihar Imo.

Jaridar Sun ta ruwaito cewa wata majiya daga yankin ta bayyana cewa an fara fafatawar ne da karfe 6 na safiyar ranar Talata yayin da ‘yan bindigar ke tursasa aiwatar da umarnin zama a gida na IPOB tare da killace hanyoyi, inda suka umurci mutane da su koma gidajensu.

Kara karanta wannan

Rikicin Goje da Inuwa: Kotu ta tasa keyar hadimin Goje zuwa kotu saboda yin rubutu a Facebook

Taswirar jihar Imo
‘Yan bindiga da Sojojin Najeriya sun yi musayar wuta a Imo kan umarnin zama a gida | Hoto: channelstv.com
Asali: UGC

Majiyar ta ce daga baya sojoji sun tunkare su inda suka mayar da martani cikin gaggawa don dakile umarnin na zama a gida.

Har zuwa lokacin wannan rahoto, ba a bayyana ko an samu asarar rayuka daga bangarorin biyu ba, kamar yadda SaharaReporters ta tattaro.

Idan dai za a iya tunawa a jiya ne kungiyar IPOB ta bukaci al’ummar yankin Kudu maso Gabas da su kara yin addu’o’in samun zaman lafiya a shiyyar, a sako Nnamdi Kanu ba tare da wani sharadi ba, da kuma tabbatar da kasar Biafra.

Duk da cewa wata sanarwa da kakakin kungiyar Emma Powerful ta fitar ba ta bayar da umarnin a zauna a gida ba, amma ta bukaci jama’a da su kulle shagunansu na wani dan lokaci a yayin da ake gudanar da addu'o'in, sannan su bude bayan kammalawa.

Kara karanta wannan

An bindige jami'in gidan yari da wasu mutane 10 a harin gidan yarin Jos

Sabon hari a Jos: 'Yan bindiga sun bude wa mazauna wuta a kauyen Durbi

A wani labarin, an harbe wasu mutane biyu mazauna kauyen Durbi da ke gundumar Shere a karamar hukumar Jos ta Gabas a jihar Filato yayin da suke fafatawa da masu garkuwa da mutane.

Maharan, a cewar mazauna garin, sun bude wuta kan mutanen da ke bibiyarsu daga maboyarsu.

Wasu da dama kuma an ce sun samu raunuka a lamarin. Wadanda suka mutun dai sun hada da Peter Inyam da Arin Kaze.

Asali: Legit.ng

Online view pixel