Kaduna-Abuja: 'Yan sanda sun yi ram da 'yan bindiga 32, sun samo motoci 17 da AK47 19

Kaduna-Abuja: 'Yan sanda sun yi ram da 'yan bindiga 32, sun samo motoci 17 da AK47 19

  • Jami’an hukumar ‘yan sanda sun kama mutane 32 da ake zargin shu’uman ‘yan ta’adda ne da ke fadin wasu jihohi
  • Ana zarginsu da garkuwa da mutane, fashi da makamai, mallakar makamai da bisa ka’ida ba, sata, harkar miyagun kwayoyi da sauransu
  • Cikinsu akwai mutane 6 ake zargin sun addabi jihar Nasarawa, Port-Harcourt, Abuja, Kebbi da jihar Zamfara inda aka kama su da satar motoci lokuta daban-daban

Jami’an hukumar ‘yan sandan Najeriya sun kama mutane 32 da ake zargin sun aikata laifuka daban-daban, ciki har da garkuwa da mutane, fashi da makamai, sumogal din makamai, mallakar makamai ba bisa ka’ida ba, harkar miyagun makamai, sata, fyade da sauransu.

‘Yan sandan sun samu nasarar amsar miyagun makamai kamar bindiga kirar AK47 guda 19, kananun bindigogi da sauran miyagun makamai. Sannan sun samu nasarar amsar motocin sata guda 17 daga wurinsu bayan bincike mai tsanani akan laifukan, Vanguard ta ruwaito.

Kara karanta wannan

'Yan bindiga sun sace basarake da matarsa da mutane da dama a Katsina

Kaduna-Abuja: 'Yan sanda sun yi ram da 'yan bindiga 32, sun samo motoci 17 da AK47 19
Kaduna-Abuja: 'Yan sanda sun yi ram da 'yan bindiga 32, sun samo motoci 17 da AK47 19. Hoto daga Vanguardngr.com
Asali: UGC

Cikinsu akwai mutane 6 da suka shahara wurin sace-sace inda aka gano sun saci motoci 6 daga wurare daban-daban ciki har da Nasarawa, Port-Harcourt, Abuja, Kebbi da jihar Zamfara.

Vanguard ta ruwaito cewa, jami’in hulda da jama’an hukumar, CP Frank Mba ya ce :

“Wadanda ake zargin suna yin sumogal da motocin da suka sata ta iyakokin kasa inda suke kai wa Alhaji Garba da ke jamhuriyar Nijar.
“Bincike ya nuna yadda wadanda ake zargin suke yin kwace, fashin motoci da bindiga kuma sukan sace mota daga taro kamar na coci, masallaci ko silma.”

Har ila yau Jami’an STS sun samu nasarar kama wasu ‘yan ta’addan daga cikin ‘yan bindigan da ke dajin Saminaka a jihar Kaduna.

Bincike ya bankado Dayyabu Mohammed a matsayin mai sayar wa manyan ‘yan bindiga da makamai ga ‘yan bindigan da ke arewa maso yamma da arewa ta tsakiya.

Kara karanta wannan

Dubun wasu gawurtattun yan bindiga 32 ya cika, yan sanda sun kwato muggan makamai

Manyan ‘yan bindigan sun hada da Yellow da Budderi. An kama Dayyabu Mohammed ne a hanyarsa ta kai makamai Jos, jihar Filato a wata motarsa kirar Golf-3, zuwa wata maboyar ‘yan bindiga da ke Birnin Gwari a jihar Kaduna.

‘Yan sandan sun kuma kama wadanda ake zargin su da kai wa matafiya a daidai wuraren Tafa, hanyar Kaduna zuwa Abuja, farmaki.

Kotun Abuja ta ayyana 'yan bindiga matsayin 'yan ta'adda

A wani labari na daban, babban kotun tarayya ta Abuja ta bayyana kungiyoyin `yan bindiga da ke barna a fadin kasar nan a matsayin 'yan ta'addan.

Daily Trust ta ruwaito cewa, Mohammad Abubukar, daraktan gurfanarwa (DPP) a ma'aikatar shari'a wanda ya shigar da karar, yace:

"Shugaba Muhammadu Buhari ya amince da matakin da ya dauka,wanda babban dalilin hakan shine ganin bayan kungiyoyin `yan bindiga da `yan ta'adda da sauran kungiyoyin ta'addanci a kasar."

Kara karanta wannan

Jami'an NDLEA sun yi ram da tsohuwa mai shekaru 70 dauke da miyagun kwayoyi

Asali: Legit.ng

Online view pixel