'Yan bindiga sun sace basarake da matarsa da mutane da dama a Katsina

'Yan bindiga sun sace basarake da matarsa da mutane da dama a Katsina

  • A ranar Litinin da dare ne ‘yan bindiga su ka afka wani kauye inda su ka yi garkuwa da dagaci, matarsa da wasu mutane da dama
  • Sun yi garkuwa da dagacin kauyen Fankama, Ahmed Saidu da ke karkashin karamar hukumar Faskari a cikin jihar Katsina
  • Majiyoyi da dama sun tabbatar da cewa babu wanda su ka halaka sakamakon farmakin da su ka kwashe sa’o’i biyu a cikin kauyen

Katsina - Wasu ‘yan bindiga sun yi garkuwa da dagacin kauyen Fankama, Ahmed Saidu, tare da matarsa da sauran mazauna kauyen da dama sakamakon wani farmaki da su ka kai da daren Litinin.

Kauyen Fankama ya na karkashin karamar hukumar Faskari ne da ke jihar Katsina.

Katsina: ‘Yan bindiga sun sake garkuwa da wani dagacin kauye
Taswirar Jihar Katsina. Hoto: The Nation
Asali: Twitter

Shin kana da labarin da ka/ki ke son an wallafa ma ka/ki? Ka tuntubemu a info@corp.legit.ng!

Kara karanta wannan

Yan bindiga da Sojojin sun yi musayar wuta a Imo kan umarnin zama a gida na IPOB

Majiyoyi da dama sun sanar da Premium Times cewa babu asarar rai ko daya da aka yi sakamakon harin da aka kwashe sa’o’i biyu ana yi.

Har yanzu ba a ji komai ba daga wurin masu garkuwa da mutanen

Bahisulhaq Alhassan, dan uwan basaraken, ya sanar da Premium Times a Katsina cewa a ranar Talata an kwashe sauran iyalan dagacin kauyen daga kauyen.

A cewarsa:

“Har yanzu ba mu ji daga gare su ba (masu garkuwa da mutanen), sai dai mu na fatan ko wasika su turo wa mutane don a san abinda za ayi.”

Habib Daudawa, wani mazaunin yankin da ke jihar Katsina ma ya kara tabbatar da harin.

Kakakin rundunar ‘yan sandan jihar, Gambo Isa bai bayar da martani akan sakon da aka tura masa ba, sannan bai yi tsokaci ga sakon WhatsApp din da Premium Times ta tura masa ba.

Buhari ga jami'an tsaro: Bana son sake jin motsin ƴan bindigan hanyar Kaduna zuwa Abuja

Kara karanta wannan

Da Duminsa: 'Yan bindiga sun bude wa motar kwamishina wuta a Kogi

A wani labarin, shugaban kasa Muhammadu Buhari ya umarci shugabannin tsaron kasar nan da su kawo karshen ta’addancin da ke aukuwa a kasa musamman a hanyar Abuja zuwa Kaduna.

Ministan harkokin cikin gida, Rauf Aregbesola ya sanar da hakan a ranar Alhamis bayan wani taro da shugaban kasa ya yi da kwamitin tsaron kasa, NSC a fadarsa da ke Abuja, Daily Trust ta ruwaito.

A cewarsa shugaban kasan ya ba ‘yan sanda da duk wasu jami’an tsaro ciki har da jami’an binciken sirri umarnin kada su zauna har sai sun kawo karshen ta’addanci, rashin tsaro, amsar kudaden fansa da sauransu a Najeriya.

Asali: Legit.ng

Online view pixel