Kotun Abuja ta ayyana 'yan bindiga matsayin 'yan ta'adda

Kotun Abuja ta ayyana 'yan bindiga matsayin 'yan ta'adda

  • Wata babbar kotun tarayya da ke Abuja ta ayyan 'yan bindiga a matsayin 'yan ta'adda a dukkan fadin kasar nan
  • Kamar yadda alkalin kotun ya bayyana, barnar da suke tafkawa ta kashe-kashe, satar shanu da sauran tada zaune tsaye ce ta sa haka
  • Alkalin kotun ya yi kira ga gwamnatin tarayya da ta hanzarta ayyana 'yan bindiga a matsayin 'yan ta'adda a kasar nan

Abuja - Babban kotun tarayya ta Abuja ta bayyana kungiyoyin `yan bindiga da ke barna a fadin kasar nan a matsayin 'yan ta'addan.

Daily Trust ta ruwaito cewa, Mohammad Abubukar, daraktan gurfanarwa (DPP) a ma'aikatar shari'a wanda ya shigar da karar, yace:

Kotun Abuja ta ayyana 'yan bindiga matsayin 'yan ta'adda
Kotun Abuja ta ayyana 'yan bindiga matsayin 'yan ta'adda. Hoto daga dailytrust.com
Asali: UGC
"Shugaba Muhammadu Buhari ya amince da matakin da ya dauka,wanda babban dalilin hakan shine ganin bayan kungiyoyin `yan bindiga da `yan ta'adda da sauran kungiyoyin ta'addanci a kasar."

Kara karanta wannan

Kotu ta haramta wa EFCC gurfanar da Dickson, ta ce CCB sun tantance kadarorinsa

A wata takardar karfafawa da ta fito daga gwamanatin tarayyan data kunsa rahotanni akan harkar tsaro, sun tabbatar da cewa kungigoyin `yan bindigan ne ke da alhakin kashe- kashe, garkuwa da mutane gami da fyade da sauran munanan ayyuka a arewa maso gabas da arewa da sauran bangarorin kasar.

An zargi kungiyoyin da alhakin assasa ta'addanci, cigaba da garkuwa da mutane tare da bukatar wani kaso na dukiya, satar mata domin aure da satar yaran makaranta da sauran mutanen kasa.

A lokacin gudanar da shari'a a ranar Alhamis, kotu ta bayyana ayyukan kungiyoyin`yan bindiga da `yan ta'adda da sauran kungiyoyin da suka kunshi nau'in ta'addanci a sasanni kasar, musamman a arewa maso kudu da arewancin kasar a matsayin nau'in ta'addanci da karya doka.

Kara karanta wannan

N2.3tr muka ware don rabawa yan Najeriya kayan tallafin Korona, Gwamnatin tarayya

Kotun ta yi Alawadai da ayyukan kungiyoyin da makamantansu a kowanne sassan kasar, ko a kungiya ko a ware da sunan koma me suke amfani da shi.

Kotun ta bukaci gwamnatin tarayya da ta ayyana `yan bindiga a matsayin `yan ta'adda da kan ta, TheCable ta ruwaito.

Bayanan Sirri: Boko Haram ne ke kai hare-haren babbar hanyar Kaduna zuwa Abuja

A wani labari na daban, bincike ya bayyana cewa hare-haren da ake yawan kai wa babban titin Abuja zuwa Kaduna duk ‘yan Boko Haram ne suke kai farmakin, kamar yadda Daily Nigerian ta ruwaito.

A ranar Lahadi, ‘yan bindiga sun yi garkuwa da matafiya da ba a san yawansu ba sannan sun halaka wani fitaccen dan siyasan jihar Zamfara, Sagir Hamidu a wani wuri mai suna Kurmin Kare a kan hanyar.

‘Yan ta’addan sun kara komawa kusa da wurin sannan suka kara budewa wasu matafiya wuta har suka yi garkuwa da wasu.

Kara karanta wannan

Labari mai dadi: Sanatoci sun nemi a karawa 'yan NYSC kudin alawus din abinci

Asali: Legit.ng

Authors:
Aisha Khalid avatar

Aisha Khalid (Hausa editor) Aisha Khalid marubuciyar jaridar Legit.ng ce mai fatan shahara. Ta samu digirinta na farko a jami'ar Ahmadu Bello da ke Zaria a shekarar 2018. Ta kwashe shekaru tana rubutu a fannonin siyasa, nishadi, tsegumi da sauransu. Za a iya tuntubar ta a adireshin email din ta kamar haka: aisha.khaleed@corp.legit.ng

Online view pixel