Bayani Dalla-Dalla: Yadda zaka cike fom din shiga aikin dan sanda a yanar gizo 2021 da aka fara yau

Bayani Dalla-Dalla: Yadda zaka cike fom din shiga aikin dan sanda a yanar gizo 2021 da aka fara yau

  • Hukumar yan sandan kasar nan, ta sanar da bude shafin yanar gizo domin ɗaukar sabbin ma'aikata 2021
  • Mun tattaro muku duk takardun da ake bukata da kuma bayani kan yadda zaka cike fom ɗin ba tare da kuskure ba
  • Hukumar ta kuma baiwa yan Najeriya masu sha'awar shiga aikin makonni shida su kammala cike bayanan su, su tura mata kai tsaye

Abuja - Hukumar yan sandan ƙasar nan ta bude shafin yanar gizo domin ɗaukar sabbin jami'an yan sanda na shekarar 2021 ranar Litinin 29 ga watan Nuwamba.

Wannan na kunshe a wata sanarwa da hukumar ta fitar a shafinta na Facebook ɗauke da sa hannun kakakinta, Frank Mba.

Sanarwan wacce akaiwa take da 'Ɗaukar sabbin jami'an yan sanda 2021,' Hukumar tace waɗan da suka samu nasara zasu zama sabbin yan sanda.

Kara karanta wannan

Dubun wani kasurgumin dan fashi da ake nema ruwa a jallo ya cika a jihar Kano

Aikin ɗan sanda
Damar Aiki: Hukumar yan sanda ta bude shafin yanar gizo na ɗaukar dabbin ma'aikata 2021 yau Hoto: Nigerian Police Force
Asali: Facebook

Neman shiga aikin ɗan sanda a shafin da hukumar yan sanda ta buɗe zai shafe makonni 6, fara wa daga yau Litinin 29 ga watan Nuwamba, 2021.

Shin kana da labarin da ka/ki ke son an wallafa ma ka/ki? Ka tuntubemu a info@corp.legit.ng!

Bayan mutane sun kammala cike fom din shiga aikin, hukumar zata gayyaci waɗan da suka samu nasara zuwa wurin tantancewa daga 10 zuwa 24 ga watan Janairu.

Abubuwan da ake bukata

Legit.ng Hausa ta tattaro muku takardun da ake bukatar kowane mai neman aikin dan sanda ya tabbata ya mallaka

1. Lambar katin zama ɗan ƙasa (NIN), adireshin tura sako na Email wanda ke aiki, da lambar wayar salula.

2. Ya zama wajibi kana da mafi karanci credits 5 a zaman jarabawar gama sakandire da bai wuce biyu ba na WASSCE/GCE/NECO/NABTEB. Amma dole ne ka ci Turanci da Lissafi.

3. Kwafin takardan kammala sakandiren ka na asali zaka saka a shafin yanar gizo.

Kara karanta wannan

Zamfara: An kama wata mata da harsashi 991 na AK-47 za ta kai wa hatsabibin shugaban ƴan ta'adda

4. Wajibi mai neman aiki kada ya gaza shekara 17 kuma kada ya wuce shekara 25.

5. Wajibi ne duk mai neman aikin ya kasance mai cikakkiyar lafiya ta fili da ta boye. Kuma namiji kada ya gaza tsawon mita 1.67m, mata kuma sai kin kai tsawon mita 1.64 zuwa sama.

Dall-Dalla yadda zaka cike fom ɗin neman aikin

Da zaran ka kammala haɗa waɗan can abubuwan da muka zayyana a sama, sai ka ziyarci shafin www.policerecruitment.gov.ng, ka cike fom ka tura.

Ya zama wajibi ga duk mai neman aiki ya sake duba duk bayanan da ya cike a fom ɗin kafin ya tura domin guje wa kuskure da saka bayanai ba dai-dai ba.

Bayan kammala cike fom da tura wa hukumar yan sanda kai tsaye ta yanar gizo, kowane mai neman aikin zai fito da fom ɗin wanda zai tsaya masa, kuma ya tabbata yaje da su wurin tantancewar fili.

Kara karanta wannan

Da Duminsa: An harbe kasurgumin dan bindigan da ya jagoranci sace matafiya a hanyar Kaduna-Abuja

A wani labarin na daban kuma mun kawo muku bayani Dalla-Dalla kan Jerin matakan da zaka bi, ka mallaki gida a saukake a shirin cefanar da gidaje na FG

A ranar Jumu'a 12 ga watan Nuwamba, Gwamnatin tarayya ta sanar da bude shafin intanet domin siyar da gidaje ga yan Najeriya.

Ministan ayyuka da gidaje, Babatunde Fashola, yace jihohi 34 da babban birnin tarayya Abuja zasu samu damar shiga shafin.

Asali: Legit.ng

Online view pixel