Dubun wani kasurgumin dan fashi da ake nema ruwa a jallo ya cika a jihar Kano

Dubun wani kasurgumin dan fashi da ake nema ruwa a jallo ya cika a jihar Kano

  • Rundunar yan sanda reshen jihar Kano ta samu nasarar cafke wani ɗan fashi da ake nema ruwa a jallo mai suna, Sabitu Ibrahim
  • Rahotanni sun bayyana cewa ɗan fashin yaro ne dan shekara 18, amma ya addabi mutane da aikata fashi da makami a jihar
  • Kakakin yan sandan jihar, DSP Abdullahi Haruna, yace an kuma kame wasu mutum biyu dake siyan kayan sata

Kano - Wani kasurgumin ɗan fashi da makami, ɗan kimanin shekara 18, Sabitu Ibrahim, wanda yana cikin jerin waɗan da yan sanda ke nema, ya shiga hannu a Kano.

Vanguard tace kakakin rundunar yan sanda reshen jihar Kano, DSP Abdullahi Haruna, shine ya tabbatar da nasarar ga manema labarai.

Ya kuma kara da cewa hukumar yan sanda ta damke wasu mutum biyu dake siyan kayayyakin sata a jihar.

Kara karanta wannan

Gwarazan yan sanda sun hallaka kasurgumin ɗan bindiga a Hotel ɗin jihar Kaduna

Yan sanda
Dubun wani kasurgumin dan fashi da ake nema ruwa a jallo ya cika a jihar Kano Hoto: dailypost.ng
Asali: UGC

A wata sanarwa da ya fitar, DSP Haruna yace:

Shin kana da labarin da ka/ki ke son an wallafa ma ka/ki? Ka tuntubemu a info@corp.legit.ng!

"A ranar 24 ga watan Nuwamba, 2011 da misalin ƙarfe 11:30 na safe, jami'an yan sanda na Operation Puff Ander bisa jagoranci Buba Yusuf, yayin da suka fita sinitiri cikin kwaryar birnin Kano, sun damke dan fashi mai hatsari Sabitu Ibrahim."
"Wanda aka fi sani da 'Aljan' ɗan kimanin shekara 18 daga kauyen Kaburma yankin karamar hukumar Dawakin Tofa a jihar Kano."
"Aljan na ɗaya daga cikin jerin mutanen da rundunar yan sandan Kano take nema ruwa a jallo bisa zargin aikata fashi da makami da dama a faɗin jihar."

Mutanen sun amsa laifin su

Kakakin yan sandan ya bayyana cewa waɗan da aka kame ɗin sun amsa laifin da ake zarginsu da aikatawa yayin bincike.

"Yayin gudanar da bincike wanda ake zargi ya amsa laifin cewa sun haɗa kai da wasu wajen farmakan direban adedeta sahu, inda suka yi kokarin kashe shi amma ya tsira da raunuka."

Kara karanta wannan

Zamfara: An kama wata mata da harsashi 991 na AK-47 za ta kai wa hatsabibin shugaban ƴan ta'adda

"Amma sun samu nasarar awon gaba da Keke Napep dinsa. Da aka tsananta bincike an kama wasu mutun biyu Abdullahi Suleiman da Abubakar Muhd."
"Mutanen sun amsa cewa sun sayi wasu sassan keken adedeta sahu daga hannun Aljan."

A wani labarin na daban kuma Sojoji sun hallaka dandazon yan bindiga da suka addabi hanyar Kaduna-Abuja

Jami'an tsaro sun samu nasarar hallaka yan bindiga da dama dake garkuwa da mutane a hanyar Kaduna zuwa Abuja.

Rahotanni sun bayyana cewa hukumomin tsaro sun fara jibge jami'ansu a kan hanyar, bayan umarnin shugaba Buhari.

Asali: Legit.ng

Online view pixel