Nasarun Minallah: An harbe kasurgumin dan bindigan da ya jagoranci sace matafiya a hanyar Kaduna-Abuja

Nasarun Minallah: An harbe kasurgumin dan bindigan da ya jagoranci sace matafiya a hanyar Kaduna-Abuja

  • Jami'an tsaro sun hallaka kasurgumin ɗan bindigan da ya jagoranci sace matafiya da dama a hanyar Kaduna-Abuja
  • Rahotanni sun bayyana cewa jami'an hukumar yan sanda ne suka wa tawagarsa kwantan bauna yayin da suka je siyan barasa
  • Gwamnatin jihar Kaduna ta sanar da ɗage dokar hana amfani da sabis a wasu yankunan jihar

Kaduna - Wani kasurgumin ɗan bindiga da ake zaton shine ya jagoranci harin kan hanyar Kaduna zuwa Abuja ranar Lahadi, ya bakunci lahira.

Dailytrust ta rahoto cewa maharan sun sace matafiya da yawan gaske, yayin da suka hallaka jigon APC a Zamfara a harin da suka fara ranar Lahadi.

Yan bindigan sun kwashe kwanaki hudu suna kai hari a lokuta daban-daban a kan hanyar, kamar yadda Vanguard ta ruwaito.

Yan bindiga
Nasarun Minallah: An harbe kasurgumin dan bindigan da ya jagorance sace matafiya a hanyar Kaduna-Abuja Hoto: punchng.com
Asali: UGC

Ta ya aka kashe ɗan bindigan?

Kara karanta wannan

Cikakken Bayani: Gwamna El-Rufa'i ya dage dokar hana amfani da hanyoyin sadarwa a jihar Kaduna

Wata majiya daga cikin jami'an tsaro, ya bayyana cewa shugaban tawagar yan bindiga ya sha alburushi ne a wata musayar wuta da jami'an yan sanda.

Rahotanni sun bayyana cewa an gano sunansa, Yellow Baba Arusa, kuma jami'an sun kwato mashin da kuma bindiga da ake zargin na tawagar ne.

Jami'an tsaro ne suka yi wa tawagar yan bindigan kwantan bauna a ƙaramar hukumar Kaduna ta kudu, yayin da yan bindigan suka je siyan barasa.

Gwamnati ta ɗage dokar hana amfani da sabis

A ranar Jumu'an nan da muke ciki, gwamnatin jihar Kaduna ta dage dokar datse hanyoyin sadarwa da ta kakaba na wata uku a wasu yankunan jihar.

Legit.ng Hausa ta tattaro muku cewa gwamnatin jihar ta ɗauki wannan matakin ne biyo bayan yawaitar harin yan bindiga musamman a hanyar Kaduna-Abuja.

Kara karanta wannan

Tashin Hankali: An tsinci gawar wani mutumi mai aure, da wata Amarya a cikin mota a Kano

A baya dai gwamnatin Kaduna ta umarci hukumar NCC ta datse sabis a wasu yankunan jihar bayan hukumomin tsaro sun bukaci hakan.

A wani labarin na daban kuma yan binidga sun gargaɗi iyalan dan sanda cewa su gaggauwa kawo miliyan N200m kafin su bar wurin sabis

Yan bindigan da suka sace matafiya a kan hanyar Kaduna zuwa Abuja sun nemi iyalan wani ɗan sanda su biya fansa.

Rahoto ya bayyana cewa maharan sun nemi a tattara musu miliyan N200 cikin awanni 6 kafin su bar gurin sabis.

Asali: Legit.ng

Authors:
Ahmad Yusuf avatar

Ahmad Yusuf (Hausa editor) Ahmad Yusuf ma'aikacin jaridar Legit.ng sashin Hausa ya fara aiki a 2021, ya kware wajen kawo labarai da rahotanni da suka shafi siyasa da al'amuran yau da kullum. Matashin ɗan jaridar ya koyi Lissafi a digirinsa na farko a Jami'ar Kimiyya da Fasaha da ke Wudil, Kano (KUST) ya kuma samu shaidar kwarewa a fannin aikin jaridar zamani daga Reuters a 2022. Kafin fara aiki da Legit Ahmad ya yi aiki da jaridu da dama na turanci da Hausa tun 2012. Mail: ahmad.yusuf@corp.legit.ng 07032379262

Online view pixel