Mutum daya ya mutu, yayin da wasu miyagun yan bindiga suka kai sabon hari rugar Fulani a Kaduna

Mutum daya ya mutu, yayin da wasu miyagun yan bindiga suka kai sabon hari rugar Fulani a Kaduna

  • Wasu miyagun yan bindiga sun bi tsakar dare sun kai hari wata Rugar Fulani a yankin Igabi ta jihar Kaduna
  • Rahotanni sun bayyana cewa maharan sun kashe mutum ɗaya yayin harin, kuma sun sace adadi mai yawa na dabbobi
  • Dagacin yankin, Alhaji Abdullahi, ya tabbatar da lamarin, yace zai je rugar domin tabbatar da abinda ya faru

Kaduna - Wasu tsagerun yan bindiga sun farmaki rugar Fulani a yankin Barakallahu, ƙaramar hukumar Igabi, jihar Kaduna.

Dailytrust ta rahoto cewa maharan sun hallaka mutum ɗaya, wanda aka gano sunansa, Imam Abubakar.

Haka nan kuma yan bindigan sun kwashi adadi mai yawa na shanun Fulanin, sun yi awon gaba da su.

Yan bindiga
Mutum daya ya mutu, yayin da wasu miyagun yan bindiga suka kai sabon hari rugar Fulani a Kaduna Hoto: punchng.com
Asali: UGC

Yadda lamarin ya faru

Dagacin yankin, Alhaji Muhammad Abdullahi, shine ya tabbatar da faruwar lamarin ga manema labarai.

Kara karanta wannan

Karin bayani: Yan bindiga sun faɗa tarkon jami'an tsaro yayin da suka kai hari gidan yari a Jos

Ya kuma bayyana cewa maharan sun mamaye rugar ne da misalin kare 12:15 na tsakar daren ranar Lahadi.

Alhaji Abdullahi yace:

"Da tsakiyar dare, muka fara jiyo ƙarar harbin bindiga, kuma muna tsammanin sun harba bindiga aƙalla sau 50 kafin su fice daga rugan."
"An sanar da ni cewa sun kashe mutum ɗaya kuma sun yi awon gaba da dabbobi amma har yanzun ba'a tabbatar da adadin su ba. Yanzu ina kan hanyar zuwa wurin."

A baya-bayan nan dai yan bindiga na cigaba da cin karen su babu babbaka a wasu yankunan jihar Kaduna.

Hakan yasa gwamnatin jihar ta bayyana cewa ta umarci a dawo da hanyoyin sadarwa da wasu kananan hukumomin jihar.

Wannan dai ya biyo bayan harin da yan bindiga suka kai kan matafiya a hanyar Kaduna zuwa Abuja, wanda suka shafe kwanaki hudu.

Kara karanta wannan

Gwarazan yan sanda sun hallaka kasurgumin ɗan bindiga a Hotel ɗin jihar Kaduna

A wani labarin na daban kuma Sabon Jirgin yaƙin Super Tucano ya ragargaji mayaƙan Boko Haram/ISWAP 26 a Gajiram

Rundunar sojin Operation Haɗin Kai ta samu nasarar hallaka yan ta'addan Boko Haram da ISWAP da yawa a Gajiram jihar Borno.

Rahotanni sun bayyana cewa dakarun sojin sun yi luguden wuta kan yan ta'addan yayin da suka yi yunkurin kai farmaki.

Asali: Legit.ng

Online view pixel