Nasara daga Allah: Sabon Jirgin yaƙin Super Tucano ya ragargaji mayaƙan Boko Haram/ISWAP 26 a Gajiram

Nasara daga Allah: Sabon Jirgin yaƙin Super Tucano ya ragargaji mayaƙan Boko Haram/ISWAP 26 a Gajiram

  • Rundunar sojin Operation Haɗin Kai ta samu nasarar hallaka yan ta'addan Boko Haram da ISWAP da yawa a Gajiram jihar Borno
  • Rahotanni sun bayyana cewa dakarun sojin sun yi luguden wuta kan yan ta'addan yayin da suka yi yunkurin kai farmaki
  • Hafsan soji, Janar Farouk Yahaya, ya roki sojojin kada su yi ƙasa a guiwa, su tabbata sun kakkabe ragowar yan ta'addan

Borno - Dakarun sojin sama da na ƙasa na rundunar Operation Hadin Kai sun ragargaji yan ta'addan Boko Haram da ISWAP a wani luguden wuta ta sama.

Sojojin sun kaddamar da harin bama-bamai kan yan ta'addan a Gajiram, karamar hukumar Nganzai, jihar Borno ranar Lahadi 28 ga watan Nuwamba, 2021.

Wannan na ƙunshe ne a wata sanarwa da hukumar soji ta fitar a shafin Facebook ɗauke da sa hannun kakakinta, Onyema Nwachukwu.

Kara karanta wannan

Luguden wuta: Sojoji sun hallaka yan ta'adda 90, sun damke kasurgumi da suke nema ruwa a jallo

Jirgin yakin Super Tucano
Nasara daga Allah: Sabon Jirgin yaƙin Super Tucano ya ragargaji mayaƙan Boko Haram/ISWAP 26 a Gajiram Hoto: ripplesnigerian.com
Asali: UGC

Sojojin sun yi luguden wuta kan yan ta'addan yayin da suka yi yunkurin kai farmaki sansanin soji da motocin yaki da wasu manyan makamai.

Shin kana da labarin da ka/ki ke son an wallafa ma ka/ki? Ka tuntubemu a info@corp.legit.ng!

Sojoji sun kwato makamai

Kakakin sojin ya cigaba da cewa yan ta'addan sun tsere da raunuka a jikinsu kasancewar sojoji sun kashe su da yawa kuma sun lalata kayan aikin su.

Yace:

"Sojojin sun bi sawun yan ta'addan da suka tsere kuma zuwa yanzun sun kwato makamai da suka haɗa da bindigun AK-47 guda 10, bindigar kakkaɓo jirgi guda ɗaya, Alburusai 62 da sauran su."
"Haka nan kuma an gano ƙonannun gawarwakin yan ta'addan a kan hanyar da suka bi. Amma abin takaicin shine sojoji biyu sun kwanta dama yayin gwabzawar."

COAS ya yaba wa sojojin

Shugaban rundunar sojojin ƙasa, Janar Farouk Yahaya, ya roki dakarun sojin kada su gajiya su cigaba da matsawa ragowar yan ta'adda lamba har sai sun kawo karshen su.

Kara karanta wannan

Nasrun minallah: Jirgin yakin sojoji ya yi luguden wuta kan masu karban haraji na kungiyar ISWAP a Borno

A wani labarin na daban kuma kun ji cewa An harbe kasurgumin dan bindigan da ya jagoranci sace matafiya a hanyar Kaduna-Abuja

Rahotanni sun bayyana cewa jami'an hukumar yan sanda ne suka wa tawagarsa kwantan bauna yayin da suka je siyan barasa a cikin Kaduna.

Yan bindigan sun kwashe kwanaki hudu suna kai hari a lokuta daban- daban a kan hanyar Kaduna zuwa Abuja.

Asali: Legit.ng

Online view pixel