Da Dumi-Ɗuminsa: Karar harbe-harbe na cigaba da tashi a gidan yarin Jos

Da Dumi-Ɗuminsa: Karar harbe-harbe na cigaba da tashi a gidan yarin Jos

  • Rahotanni sun bayyana cewa an jiyo karar harbe-harben bindiga a gidan gyaran hali dake Jos, babban birnin Filato ranar Lahadi
  • Jami'in yaɗa labarai na rundunar sojin Operation Safe Haven, Mejo Ishaku, yace yanzun haka jami'an rundunarsu sun kai ɗauki
  • Ana tsammanin wasu tsagerun yan bindiga ne suke kokarin fasa gidan yarin amma jami'an tsaro sun tarbe su

Jos, plateau - Jaridar Dailytrust ta rahoto cewa yan bindigan da suka kai harin gidan yari a Jos sun shiga tarkon jami'an tsaro.

Mun kawo muku rahoto cewa tun da misalin ƙarfe 5:30 na yamma ne akaji ƙarar harbe-harbe daga gidan yarin, wanda ke tsakiyar birnin Jos.

Yan bindigan sun farmaki gidan ne da adadi mai yawa, inda suka bude wuta kan jami'an dake bakin aiki har suka samu shiga ciki.

Kara karanta wannan

Jami'an tsaro sun titsiye 'yan bindigan da suka je balle gidan yarin Jos a cikin gidan

Jihar Filato
Da Dumi-Ɗuminsa: Karar harbe-harbe na cigaba da tashi a gidan yarin Jos Hoto: channelstv.com
Asali: UGC

Kakakin hukumar kula da gidan gyaran hali a Jos, Jeff Longdiem, ya tabbatar da lamarin a wani sako da ya aike wa maneman labarai.

Yace:

"Maharan sun farmaki wurin da misalin karfe 5:30 na yamma, inda suka fasa kofar bayan gwabzawa da jami'an dake aiki har suka shiga cikin gidan."
"Duk da sun samu nasarar shiga ciki, amma sun tsinci kansu a tsakiya yayin da hukumomin tsaro suka yi gaggawar kawo ɗauki domin taimakawa jami'an gidan yarin."
"Mun kara tura jami'an kula da gidan yari, a halin yanzun an shawo kan lamarin, domin jami'ai sun ƙarar da karfin da maharan suka zo da shi. Zamu sanar da karin bayani nan gaba."

Jami'an tsaro sun kai ɗauki

Rahoton channels tv ya nuna cewa wasu tsagerun yan bindiga ne ke kokarin kutsa kai gidan yarin, amma jami'an tsaro sun tarbe su ana musayar wuta.

Kara karanta wannan

Luguden Wuta: Sojoji sun hallaka dandazon yan bindiga da suka addabi hanyar Kaduna-Abuja

Jami'in yaɗa labarai na rundunar sojin Operation Safe Haven, Mejo Ishaku, ya tabbatar da lamarin, yace har yanzun ba'a gano su waye suka farmaki gidan yarin ba.

Ishaku ya kara da cewa jami'an rundunarsa na can yanzun haka suna fafatawa da maharan domin dakile yunkurin su.

Wannan gidan gyaran hali da ake kokarin fasawa yana tsakiyar Jos, babban birnin Filato, kuma yana kusa da hedkwatar yan sandan jihar.

Yanzun haka an tsammanin jami'an yan sanda na Division A zasu kawo ɗauki domin dakile harin, kasancewa ofishin su na kusa da wurin.

A wani labarin na daban kuma Dubun wani kasurgumin dan fashi da ake nema ruwa a jallo ya cika a jihar Kano

Rundunar yan sanda reshen jihar Kano ta samu nasarar cafke wani ɗan fashi da ake nema ruwa a jallo mai suna, Sabitu Ibrahim.

Rahotanni sun bayyana cewa ɗan fashin yaro ne dan shekara 18, amma ya addabi mutane da aikata fashi da makami a jihar.

Kara karanta wannan

Yanzu-yanzu: Ranar Litinin zamu dawo da Sabis jihar Zamfara, Matawalle

Asali: Legit.ng

Online view pixel