Gwarazan yan sanda sun hallaka kasurgumin ɗan bindiga a Hotel ɗin jihar Kaduna

Gwarazan yan sanda sun hallaka kasurgumin ɗan bindiga a Hotel ɗin jihar Kaduna

  • Rundunar yan sandan jihar Kaduna ta samu nasarar kashe wani sanannen ɗan bindiga a wani Otal dake jihar
  • Rahotanni sun bayyana cewa ɗan bindigan da tawagarsa sun buɗe wa yan sanda wuta daga isarsu, amma jami'ai suka maida martani
  • Kakakin yan sandan jihar, Muhammed Jalige, yace an yi kokarin ceto rayuwar dan bindigan domin samun wasu bayanai

Kaduna - Rundunar yan sandan jihar Kaduna ta bayyana cewa jami'anta sun samu nasarar sheke kasurgumin ɗan bindiga, Magaji Yellow, yayin wata musayar wuta a Otal na jihar.

The Cable ta rahoto rundunar tace jami'ai sun ƙashe ɗan bindigan ne a wani hari da suka kai Otal ɗin 'Sir Joe Guest House' dake Lamba 8, layin Sajo, Anguwan Maigero, Sabon Tasha a ƙaramar hukumar Chikun.

A wata sanarwa da kakakin rundunar yan sandan jihar, Muhammed Jalige, ya fitar ranar Asabar, yace lokacin da yan sanda suka isa Otal, ɗin, nan take yan bindigan suka bude musu wuta.

Kara karanta wannan

Dubun wani kasurgumin dan fashi da ake nema ruwa a jallo ya cika a jihar Kano

Yan sanda
Gwarazan yan sanda sun hallaka kasurgumin ɗan bindiga a Hotel ɗin jihar Kaduna Hoto: placng.com
Asali: UGC

Jalige ya kara da cewa hakan ya jawo musayar wuta tsakaninsu, inda yan tawagar Yellow Magaji, suka tsere da raunukan harbin bindiga a jikin su.

Yadda lamarin ya faru

Kakakin yan sandan ya bayyana cewa jami'ai sun yi gaggawar kai ɗan bindigan Asibiti bayan ya sha Alburusai, amma daga zuwa aka tabbatar da ya mutu.

Vanguard ta rahoto Jalige yace:

"Wani sanannen ɗan bindiga da ake kira Yellow Magaji, ya sha dalma a wata musayar wuta da yan sanda tare da yan tawagarsa, Yellow Ashana, da sauran su."
"An yi gaggawar ɗaukar ɗan bindigan zuwa Asibitin koyarwa na Barau Dikko domin ceto rayuwarsa, don samun wasu bayanai daga bakinsa."
"Amma ana isa Asibitin likitan da ya fara duba shi ya tabbatar da cewa ya mutu. Kafin mutuwan Yellow Magaji, yana daya daga cikin yan bindigan da suka addabi hanyar Abuja - Kaduna."

Kara karanta wannan

Luguden Wuta: Sojoji sun hallaka dandazon yan bindiga da suka addabi hanyar Kaduna-Abuja

Rundunar yan sandan ta roki mutane su taimaka mata da bayanai domin damke ragowar yan bindigan da suka tsere yayin fafatawar.

A wani labarin kuma Wata Dalibar Jami'ar BUK ta mutu tana tsaka da Sallah a dakin kwanan dalibai

Wata daliba dake ajin karshe a jami'ar Bayero dake Kano ta rasa rayuwarta a ɗakin kwanan ɗalibai bayan fama da gajeriyar rashin lafiya.

Rahotanni sun bayyana cewa, Binta Isa, ta faɗa wa abokan zaman ta a ɗaki cewa tana jin ciwan kirji, tana fara sallah ta rasu.

Asali: Legit.ng

Online view pixel