Luguden Wuta: Sojoji sun hallaka dandazon yan bindiga da suka addabi hanyar Kaduna-Abuja

Luguden Wuta: Sojoji sun hallaka dandazon yan bindiga da suka addabi hanyar Kaduna-Abuja

  • Jami'an tsaro sun samu nasarar hallaka yan bindiga da dama dake garkuwa da mutane a hanyar Kaduna zuwa Abuja
  • Rahotanni sun bayyana cewa hukumomin tsaro sun fara jibge jami'ansu a kan hanyar, bayan umarnin shugaba Buhari
  • A ranar Alhamis wurin taron majalisar koli ta tsaro, Shugaba Buhari ya umarci hafsoshin tsaro su kawo karshen ayyukan ta'addanci

Kaduna - A wani martani na musamman, jami'an tsaro sun aika dandazon yan bindiga lahira, waɗan da suka addabi matafiya a hanyar Kaduna zuwa Abuja.

Daily Nigerian ta ruwaito cewa jami'an tsaron sun ɗauki wannan matakin ne bayan umarnin da shugaba Buhari ya baiwa hafsoshin tsaro.

A wani hoton bidiyo da jaridar PRNigeria ta samu, ya nuna gawarwakin yan bindigan sama da goma.

Dakarun soji
Luguden Wuta: Sojoji sun hallaka dandazon yan bindiga da suka addabi hanyar Kaduna-Abuja Hoto: Defence Headquaters Nigeria
Asali: Facebook

Wata majiya daga jami'an tsaro, ya bayyana cewa ana cigaba da jibge jami'ai da suka haɗa da sojoji, yan sanda, da jami'an fasaha a wasu kauyuka dake kan babbar hanyar.

Kara karanta wannan

Sheikh Gumi ya bayyana yadda 'yan bindiga suka fi gwamnati son ganin karshen ta'addanci

Shin kana da labarin da ka/ki ke son an wallafa ma ka/ki? Ka tuntubemu a info@corp.legit.ng!

Wace nasara aka samu zuwa yanzu?

Jami'in yace:

"Tun kafin shugaban ƙasa ya bada umarni aka fara jibge jami'an tsaro amma umarnin yasa aka kara turo jami'ai da dama, da kayan aiki yakar yan bindigan."
"Zuwa yanzun mun kashe sama da yan bindiga 12 waɗan da suka yi kokarin tserewa da suka ga sojoji sun fara shawagi."
"Mafi yawan yan bindigan da muka kashe suna da hannu a sace matafiya na kwanan nan domin mutanen yankin sun gane fuskokin gawarwakin."

Wane uamrni shugaba Buhari ya bayar?

Legit.ng Hausa ta rahoto muku cewa a ranar Alhamis, shugaban kasa Buhari ya umarci hafsoshin tsaro su kawo karshen yan bindiga da yan ta'addan da suka hana zaman lafiya a Najeriya.

Shugaban ya ba su wannan umarnin ne a taron majalisar koli kan tsaro, ya kara da cewa kada su rintsa har sai yan Najeriya sun iya bacci cikin kwanciyar hankali.

Kara karanta wannan

Da Duminsa: An harbe kasurgumin dan bindigan da ya jagoranci sace matafiya a hanyar Kaduna-Abuja

Kazalika, shugaba Buhari ya umarci hukumomin tsaro su ƙara zage dantse wajen shawagi a kan hanyar Kaduna-Abuja domin ceto mutanen da aka sace.

A wani labarin na daban kuma An tsinci gawar wata mata mai juna biyu da Saurayinta a ban daki

Rahotanni sun bayyana cewa an gano gawarwakin wasu mutum uku a ban dakin gidan da suke zaune a Akure, jihar Ondo.

Mutanen sun haɗa da wani saurayi da masoyiyarsa ma'aikaciyar jinya mai ɗauke da juna biyu, da kuma abokin su.

Asali: Legit.ng

Online view pixel