Tashin Hankali: An tsinci gawar wata mata mai juna biyu da Saurayinta a ban daki

Tashin Hankali: An tsinci gawar wata mata mai juna biyu da Saurayinta a ban daki

  • Rahotanni sun bayyana cewa an gano gawarwakin wasu mutum uku a ban dakin gidan da suke zaune a Akure, jihar Ondo
  • Mutanen sun haɗa da wani saurayi da masoyiyarsa ma'aikaciyar jinya mai ɗauke da juna biyu, da kuma abokin su
  • Rundunar yan sandan jihar Ondo ta tabbatar da faruwar lamarin, tace a halin yanzun jami'ai sun fara bincike

Ondo - Jaridar The Nation ta ruwaito cewa an tsinci gawarwakin mutum uku a ɗakin da ake bayan gida na cikin gidansu dake Akure, jihar Ondo.

Rahotanni sun bayyana cewa mutanen su uku, masoya biyu saurayi da budurwa da kuma abokin su, ana zaton kashe su aka yi.

Kazalika an bayyana sunayen mutanen da suka hada da, Ojo Akinro, da budurwarsa Mary lgwe da kuma Lamidi Sheriff.

Ana zargin cewa makasan sun hallaka su ne, sannan suka ɓoye gawarwakinsu a ban daki domin rufa wa kan su asiri.

Kara karanta wannan

Zamfara: 'Yan bindiga sun tayar da wani ƙauye bayan sun yi wa mutum 7 kisar gilla

Masoya biyu
Tashin Hankali: An tsinci gawar masoya saurayi da budurwa mai juna biyu a ban ɗaki Hoto: tribuneonline.com
Asali: UGC

Mary, wacce ma'akaciyar jinya ce, ta rasa rayuwarta ɗauke da juna biyu. Kuma an gano gawarsu bayan kiran wayan da aka dinga musu ba su ɗagawa.

Yadda lamarin ya faru

Wani shaida ya bayyana cewa yan uwan mamatan ne suka balla kofar ban dakin suka gano gawar mutanen, kamar yadda Tribune Online ta ruwaito.

Yace:

"Wannan lamari ne na aikata kisa, waɗan da aka kashe sun bata kuma ba su ɗaga kiran wayar salula. Mun san cewa matasan yanzun suna jefa kansu cikin abubuwa da dama."
"Makasan sun shiga gidan ta ƙofar baya, suka kashe su, sannan suka tara gawarwakin a ban ɗaki domin su samu damar guduwa."
"An gano kofar baya a bude, kuma kayan aikin su, na'ura mai kwakwalwa da wayoyin su na nan yadda suke ba'a taba su ba."

Kara karanta wannan

Ana daf da yi musu yankan rago: Amotekun sun ceto makiyaya fulani 2 da wasu fulanin suka yi garkuwa da su

Hukumar yan sanda sun tabbatar

Kakakin rudnunar yan sanda reshen jihar Ondo, DSP Funmilayo Odunlami, ta tabbatar da faruwar lamarin ga manema labarai.

A cewarta:

"Wannan lamari ne na kisa, kuma tuni jami'an yan sanda suka fara bincike kan lamarin."

A wani labarin na daban kuma Dalibar Jami'ar BUK ta mutu tana tsaka da Sallah a dakin kwanan dalibai

Wata daliba dake ajin karshe a jami'ar Bayero dake Kano ta rasa rayuwarta a ɗakin kwanan ɗalibai bayan fama da gajeriyar rashin lafiya.

Rahotanni sun bayyana cewa, Binta Isa, ta faɗa wa abokan zaman ta a ɗaki cewa tana jin ciwan kirji, tana fara sallah ta rasu.

Asali: Legit.ng

Online view pixel