Sheikh Gumi ya bayyana yadda 'yan bindiga suka fi gwamnati son ganin karshen ta'addanci

Sheikh Gumi ya bayyana yadda 'yan bindiga suka fi gwamnati son ganin karshen ta'addanci

  • Sheikh Gumi ya zargi gwamnatin Najeriya da kin son a tattauna da 'yan bindiga don kawo zaman lafiya a kasar
  • Ya bayyana cewa, 'yan bindiga sun fi gwamnatin Najeriya son ganin karshen ta'addancin da ke faruwa a kasar
  • Ya kuma bayyana irin yadda take kokari don ganin an samu mafita mai kyau ta hanyar sauya ra'ayioyin kisa na 'yan bindigan

Najeriya - Sheikh Ahmed Gumi, shahararren malamin addinin Islama a Najeriya ya bayyana cewa, 'yan bindiga sun fi kaunar a kawo karshen ta'addanci fiye da gwamnati.

Malamin ya bayyana haka ne yayin wata hira da jaridar Daily Trust, inda ya bayyana kokarinsa na shawo kan 'yan bindiga domin su bar aikata barna su zauna da kowa lafiya.

Kara karanta wannan

Mun shirya tsaf domin mitsike su: Martanin FG kan ayyana 'yan bindiga matsayin 'yan ta'adda

Gumi ya daura laifukan da suke faruwa na rashin tsaro ga gwamtocin kasar nan, inda ya bayyana cewa, a cikinsu akwai wadanda suke amfana da tashe-tashen hankula shiyasa basa son batun ya kare.

Sheikh Ahmed Mahmud Gumi
Sheikh Gumi: 'Yan bindiga sun fi gwamnati son ganin karshen ta'addanci a Najeriya | Hoto: Dr Ahmad Abubakar Mahmud Gumi
Asali: Facebook

Ya kuma bayyana irin goyon bayan da yake samu daga bangarori daban-daban wajen ganin an dakatar da ayyukan ta'addanci ba tare da amfani da soja ba.

A bangare guda, Gumi ya koka kan yadda wasu mutane, ciki har da gwamnatoci ke ci gaba da sukarsa, da kuma nuna shi a matsayin mai goyon bayan ta'addanci.

Da yake amsa tambayar wakilin Daily Trust kan shirinsa na magance ta'addanci ta hanyar lallabi, Gumi ya shaida cewa:

"Na samu hadin kai da fatan alheri daga ’yan Najeriya da dama. Amma abin takaici, kuma ni ma ban yi mamaki ba, akwai mutane da yawa da suke adawa da hakan.

Kara karanta wannan

Muna goyon bayan kara farashin man fetur dari bisa dari, Yan kasuwan Mai IPMAN

"Akwai mutanen da suke farin ciki, ‘suna kashe kansu’ kuma suna son mu ci gaba.
"Ba sa so su fahimta, don haka duk wata mafita da aka ba da za su yake ta, ta hanyar kokarin sanya mafitar ta zama baka.
"Kuma akwai mutanen da kawai munanan laifukan da ‘yan bindiga ke aikatawa ke cutar da su; kashe-kashe, fyade, kwace, duk abin da suke yi, don haka abin da wadannan mutane suke so shi ne daukar fansa; duk abin da ya rage daga haka, ba sa son ji."

Da yake bayyana daya bangaren, Gumi ya ce akwai wadanda suke son rikicin ya ci gaba da faruwa, kasancewar suna samun kaso mai tsoka daga ciki.

Ya kara da cewa:

"Kuma akwai mutanen da ke amfana da rikicin, suna samun kaso mai yawa, da yawa."

Ya kamata a yafe wa 'yan bindiga

A bangare guda, malamin ya bayyana ra'ayinsa kan ci gaba da yakar 'yan bindiga, inda ya ce kamata ya yi gwamnati ta yafe musu, sannan ta daura su a kan turba mai kyau.

Kara karanta wannan

Kotun Abuja ta ayyana 'yan bindiga matsayin 'yan ta'adda

Da yake bayyana manufarsa ta cewa a yafe wa 'yan bindigan tare da sauraransu, Gumi ya bayyana yadda yake hulda dasu kuma suke jin maganarsa.

A cewarsa:

"Wannan shine manufata! Don haka, ina hulda da mutanen da suka rigaya sun zama masu taurin kai, masu yawan fushi, miyagu, jahilai, masu dauke da makamai, da shan miyagun kwayoyi suna kisa a ko'ina. Amma na san suna sauraron wani."

Hakazalika, Gumi ya musanta cewa, duk da tattaunawa da yake da 'yan bindigan akan samu yawaitar kai hare-hare, inda ya koka kan yadda gwamnati ke yaudararsa.

Ya kara da cewa:

"Don haka su [’yan bindiga] ne ke ce mani, ‘Dubi abin da muka fada maka; mutanen nan suna yaudarar ka, mutanen nan ba da gaske suke ba kuma za ka gani’ don haka na fahimci abin da suka fada gaskiya ne.
"Bari in gaya maka, nan da can mutane suna ta harbe-harbe, na ce musu ina son ganinku, ku zo mu taru mu yi magana duk suka zo. Wasu sun yi tafiya mai tsawo a kan babura na kwana biyu, shin hakan bai nuna da gaske suke ba? Amma ba zan iya kiran kowa a cikin gwamnati ba; Ba zan iya kira ba!"

Kara karanta wannan

Zamu nunawa yan Najeriya cewa PDP ta canza, Gwamnan jihar Oyo

Da yake bayyana dalilin da yasa ba zai gayyaci gwamnati ba, kuma ya bayana ra'ayin cewa 'yan bindiga sun fi gwamnati son a zauna lafiya, Gumi ya ce:

"Domin ba za su amsa ba. Don haka, wa ya fi saukin wajen son tattaunawa?"

'Yan bindiga sun dira gonar wasu mutane yayin da suke girbi, sun tafka aika-aika

A wani labarin, masu garkuwa da mutane sun kashe wani mutum mai suna Ayuba, tare da yin garkuwa da wasu ‘yan uwansa shida a cikin wata gonarsu da ke unguwar Lagbeta a karamar hukumar Kogi ta jihar Kogi.

Daily Trust ta ruwaito cewa, al’ummar Labgeta na kan hanyar Abuja zuwa Lokoja da ake yawan hada-hada.

Dan uwan ​​wadanda abin ya shafa Ishaya Bulus, ya ce lamarin ya faru ne da safiyar Laraba da misalin karfe 10:12 na safe a lokacin da dangin ke girbin amfanin gona.

Kara karanta wannan

Matasan ‘yan Najeriya 4 da suka ginawa iyayensu mata gida, daya daga cikinsu bata kai shekara 15 ba

Asali: Legit.ng

Online view pixel