Da Dumi-Dumi: Dalibar Jami'ar BUK ta mutu tana tsaka da Sallah a dakin kwanan dalibai

Da Dumi-Dumi: Dalibar Jami'ar BUK ta mutu tana tsaka da Sallah a dakin kwanan dalibai

  • Wata daliba dake ajin karshe a jami'ar Bayero dake Kano ta rasa rayuwarta a ɗakin kwanan ɗalibai bayan fama da gajeriyar rashin lafiya
  • Rahotanni sun bayyana cewa, Binta Isa, ta faɗa wa abokan zaman ta a ɗaki cewa tana jin ciwan kirji, tana fara sallah ta rasu
  • VC Farfesa Adamu Abbas, ya jajantawa iyayenta da yan uwa bisa wannan rashi, tare da fatan rahamar Allah

Kano - Wata daliba dake ajin ƙarshe a tsangayar Ilimi ta jami'ar Bayero dake Kano (BUK), Binta Isa, ta rasu a ɗakin kwanan dalibai ranar Jumu'a 26 ga watan Nuwamba, 2021.

Wannan na kunshe ne a wata sanarwa da jami'ar ta fitar a shafinta na Facebook ɗauke da sa hannun mataimakin rijistara, Lamara Garba

Ɗalibar wacce ta fito daga jihar Kogi, ta rasa rayuwarta ne da misalin ƙarfe 7:00 na dare bayan fama da gajeruwar rashin lafiya da ta danganci ciwan ƙirji.

Kara karanta wannan

Tashin Hankali: An tsinci gawar wani mutumi mai aure, da wata Amarya a cikin mota a Kano

A cewar daraktan lafiya na jami'ar, wanda ya tabbatar da aukuwar lamarin, Binta ta je Asibitin jami'a na New Campus a ranar 24 ga watan Nuwamba, inda ta yi korafin tana fama da ciwan ƙirji.

Jami'ar BUK
Da Dumi-Dumi: Dalibar Jami'ar BUK ta mutu tana tsaka da Sallah a dakin kwanan dalibai
Asali: Facebook

Shin kana da labarin da ka/ki ke son an wallafa ma ka/ki? Ka tuntubemu a info@corp.legit.ng!

Ya ƙara da cewa jami'an da suka duba mamaciyar a lokacin, sun bata magani tare da zayyana mata yadda zata yi amfani da su.

Daraktan ya bayyana cewa daga nan Binta ta samu sauki, domin ta cigaba da halartan Lakca ranar Alhamis da Jumu'a, kuma ta cigaba da ayyukan karatunta.

Yace:

"A ranar Jumu'a 26 ga watan Nuwamba, 2021 da yamma, lokacin sallar Magriba, ta shaida wa abokiyar zaman ɗakinta cewa tana jin ciwan ƙirji, amma a haka ta kokarta ta yi Alwala domin ta yi sallar Magrib a ɗakin."
"Abokan zamanta a ɗakin sun kaɗu kuma sun tsorata da suka dawo suka tarad da ita ta yi warwas a ƙasa."

Kara karanta wannan

Hanyoyi 5 da za'a ka iya kare ban dakin zamani daga macizai

"Nan take suka sanar da mutane, akai gaggawar kaita asibitin koyarwa na Aminu Kano, inda likita ya tabbatar da cewa ta rasu."

Jami'a ta sanar da iyalan dalibar

Mataimakin shugaban BUK, Farfesa Sagir Adamu Abbas, tare da rijistara, Jamil Ahmad Salim, daraktan lafiya da darakan tsaro, Abdulyakin Ibrahim duk sun halarci wurin da lamarin ya faru.

A halin yanzun jami'a ta sanar da ɗan uwan ɗalibar, wanda yake zaune a cikin garin Kano, game da lamarin da ya faru

BUK ta yi jimamin wannan rashi

VC Farfesa Adamu, a madadin jagororin BUK, malamai da ɗalibai, ya bayyana damuwarsa da rasuwar matashiya Binta Isa, wacce ta mutu ta na gab da kammala karatunta.

Ya kuma mika ta'aziyya ga iyayenta, yan uwa da abokan karatu, kuma ya yi addu'a Allah ya yafe mata kura-kuranta, ya sa tana daga cikin yan Aljanna.

A wani labarin na daban kuma An harbe kasurgumin dan bindigan da ya jagoranci sace matafiya a hanyar Kaduna-Abuja

Kara karanta wannan

Yan Najeriya sun yi martani kan wata yarinya da ta ci A a darussan WAEC, ta ci 345 a Post UTME

Rahotanni sun bayyana cewa jami'an hukumar yan sanda ne suka wa tawagarsa kwantan bauna yayin da suka je siyan barasa a cikin Kaduna.

Yan bindigan sun kwashe kwanaki hudu suna kai hari a lokuta daban- daban a kan hanyar Kaduna zuwa Abuja.

Asali: Legit.ng

Online view pixel