Jama'a na neman mafaka bayan jami'an kwastam sun bude musu wuta kan kisan abokin aikinsu

Jama'a na neman mafaka bayan jami'an kwastam sun bude musu wuta kan kisan abokin aikinsu

  • Fusatattaun jami'an hukumar kwastam ta kasa sun fada kauyen Fagbohun domin daukar fansan kisan abokan aikinsu 2
  • Jami'an sun dinga banka wa gidajen jama'a wuta, babura tare da fadawa fadar dagacin kauyen kuma suka kama wasu
  • Wasu da ake zargin 'yan sumogal ne sun kai wa jami'an farmaki a makon da ya gabata kuma suka halaka 2 daga ciki

Yewa, Ogun - Jami'an hukumar kwastam ta kasa, NCS, sun fada wani kauye da ake kira Fagbohun da ke karamar hukumar Yewa ta jihar Ogun inda suka gigita kauyen.

An zargi fusatattun jami'an kwastam din da banka wa wasu gidaje, babura tare da kakkabe fadar dagacin kauyen kuma suka cafke wasu jama'a, Daily Trust ta wallafa.

Jama'a na neman mafaka bayan jami'an kwastam sun bude musu wuta kan kisan abokin aikinsu
Jama'a na neman mafaka bayan jami'an kwastam sun bude musu wuta kan kisan abokin aikinsu. Hoto daga dailytrust.com
Source: UGC

Wannan ya biyo bayan kisan gillar da aka yi wa jami'an kwastam biyu bayan arangamar da suka yi da 'yan sumogal a makon da ya gabata.

Read also

Bincika Gaskiya: Shin hukumar 'yan sanda ta dawo da Abba Kyari bakin aiki bayan bincike?

Daily Trust ta ruwaito cewa, arangamar ta auku ne a ranar Talata da ta gabata yayin da wani jami'in da ke aiki a Federal Operating Unit (FOU), Ikeja, Legas ya isa kauyen domin aiki.

An tattaro cewa, bayan 'yan sumogal sun hango jami'an sintirin, sun dira kansu kuma aka rasa jami'ai biyu a lamarin.

Sai dai, a ranar Laraba da ta gabata, an ga gawar daya daga cikin jami'an kusa da rafin kauyen Ajegun Iyaloosa babu bindigarsa. Washegari aka sake samun gawar dayan jami'in.

Sai dai kuma, a wani farmaki da yayi kama da na daukar fansa, jami'an sun ziyarci yankin inda suka dinga cin zarafin jama'a, lamarin da yasa wasu suka dinga tserewa daga yankin.

An tsinci gawar jami'in kwastam da miyagu suka yi garkuwa da shi

Read also

Yadda Tarayyar Turai ta kashe £130m wajen tallafawa 'yan gudun hijira a Borno

A wani labari na daban, an tsinci gawar jami'in hukumar kwastam da ake sace a jihar Ogun a ranar Talata da ta gabata, Daily Trust ta wallafa.

Wasu miyagu da ake zargin 'yan sumogal ne suka yi wa jami'an kwanton bauna yayin da suka fita sintiri a karamar hukumar Yewa ta kudu da ke jihar kuma suka sace jami'ai biyu.

An tsinta gawar daya daga cikin jami'an a wani rafi kusa da kauyen Fagbohun da ke karamar hukumar a ranar Laraba.

Source: Legit.ng

Online view pixel