Mata ta sheke mijinta kwanaki bayan 'yar uwarta ta kashe nata

Mata ta sheke mijinta kwanaki bayan 'yar uwarta ta kashe nata

  • Kimanin mako guda bayan wata ta dabawa mijinta wuka a Edo, wata mata daga ahlin ta kuma kashe nata mijin
  • An tattaro cewa sabani ne ya shiga tsakanin matar mai suna Maimuna da mijinta, Mallam Nasiru Dagana inda lamarin ya kai ga har dambe ya kaure a tsakaninsu
  • A cikin haka ne sai Maimuna ta ture mijin nata inda shi kuma ya fadi ya buga kai a kasa, amma ko da aka kai shi asibiti sai yace ga garinku

Jihar Edo - Kasa da mako daya bayan wata mata ta kashe mijinta wanda ya kama ta da wani suna cin amanarsa a jihar Edo, wata mata daga wannan ahlin ta kuma kashe nata mijin.

An yi zargin cewa matar wacce aka ambata da suna Maimuna ta kashe mijinta mai suna Mallam Nasiru Dagana.

Read also

Budurwa ta gurfanar da tsohon saurayinta a gaban kotun musulunci a jihar Kaduna

Mata ta sheke mijinta kwanaki bayan 'yar uwarta ta kashe nata
Mata ta sheke mijinta kwanaki bayan 'yar uwarta ta kashe nata Hoto: Vanguard
Source: UGC

Jaridar Daily Trust ta rahoto cewa lamarin ya afku ne a karshen mako a Jattu, Uzairue, karamar hukumar Etsako ta yamma da ke jihar Edo.

Majiya ta ce a ranar da abun zai faru, marigayin ya je gona tare da matansa don yin wasu ayyuka amma bayan sun dawo, sai sabani ya shiga tsakaninsa da daya daga cikin matan nasa inda fada ya kaure.

Shin kana da labarin da ka/ki ke son an wallafa ma ka/ki? Ka tuntubemu a info@corp.legit.ng!

Sannan kuma cewa a yayin fadan, sai matar ya ture mijin nata sannan a cikin haka ya buga kai a kasa sannan ya suma.

Ya ce an kwashi marigayin zuwa asibiti cikin gaggawa don samun kulawar likitoci amma kuma bai farfado ba.

Ba a samu jin ta bakin Kontons Bello, jami’in hulda da jama’a na rundunar yan sandan jihar Edo ba saboda baya amsa kiran wayarsa.

Read also

Magidanci ya nemi kotu ta raba auren shekaru 19 saboda matarsa na 'sheƙe aya' da mai maganin gargajiya

Matar aure ta daɓa wa mijinta, Abdulateef, wuƙa ya mutu bayan ya kama ta dumu-dumu da kwarto a gidansa

A gefe guda, mun kawo a baya cewa wani magidanci mai suna Abdulateef ya riga mu gidan gaskiya bayan matarsa ta daba masa wuka.

Jaridar Daily Trust ta rahoto cewa matar ta yi wa mijin wannan raunin ne bayan ya kama ta da wani mutum a gidansu. An gano cewa lamarin ya faru ne misalin karfe 3 na dare a ranar Lahadi, a karamar hukumar Etsako na jihar Edo.

Matar ta daba wa mijinta wuka ne bayan ya dawo gida cikin dare ya kama ta da wani mutum a gadonsu.

Source: Legit Nigeria

Online view pixel