Matar aure ta daɓa wa mijinta, Abdulateef, wuƙa ya mutu bayan ya kama ta dumu-dumu da kwarto a gidansa

Matar aure ta daɓa wa mijinta, Abdulateef, wuƙa ya mutu bayan ya kama ta dumu-dumu da kwarto a gidansa

  • Wata matar aure ta yi sanadin mutuwar mijinta mai suna Abdulateef a karamar hukumar Etsako, jihar Edo
  • Matar ta halaka mijinta ne ta hanyar caka masa wuka bayan ya kama ta da wani mutum a gida
  • Majiya daga unguwar ta tabbatar da afkuwar lamarin tana mai cewa yan sanda sun kama matar

Jihar Edo - Wani magidanci mai suna Abdulateef ya riga mu gidan gaskiya bayan matarsa ta daba masa wuka.

Jaridar Daily Trust ta rahoto cewa matar ta yi wa mijin wannan raunin ne bayan ya kama ta da wani mutum a gidansu.

An gano cewa lamarin ya faru ne misalin karfe 3 na dare a ranar Lahadi, a karamar hukumar Etsako na jihar Edo.

Matar aure ta daɓa wa mijinta, Abdulateef, wuƙa ya mutu bayan ya kama ta dumu-dumu da kwarto a gidansa
Matar aure ta daɓa wa mijinta wuƙa ya mutu bayan ya kama ta dumu-dumu da wani mutum a gidansa. Hoto: Daily Trust
Asali: Twitter

Kara karanta wannan

Da Duminsa: An gano gawar ɗan jaridar Nigeria, Salem, da ya ɓace

Matar ta daba wa mijinta wuka ne bayan ya dawo gida cikin dare ya kama ta da wani mutum a gadonsu.

Majiya ta yi karin bayani

Wata majiya ta ce:

"Mutumin yana zaune da matansa biyu ne a gidansa, amma dole yasa ya kama hayar wani gidan ya saka uwargidansa domin a samu zaman lafiya yayin da shi kuma ya ke zaune da amaryar a gidansa."

Ya ce marigayin ya ziyarci uwargidansa ya kwana a can amma ana jita-jitar cewa wani mutum na zuwa ganin amaryarsa duk dare idan baya nan kamar yadda ya zo a ruwayar Daily Trust.

A cewarsa, marigayin ya dawo daga gidan uwar gidan inda ya kama mata haya, amma yana shigowa gidansa sai ya ga amaryarsa da wani mutum a uwar daka.

Marigayin ya damke mutumin ana hakan sai matar ta daba masa wuka sau biyu a cikinsa domin ya saki mutumin ya tsere domin mutane su ga kamar dan fashi ne ya zo gidan.

Kara karanta wannan

Kisan babban jami'an soja a Kaduna: Makwabcinsa ya bayyana gaskiyar wadanda suka kashe shi

Ya ce marigayin ya rasu sakamakon raunin da matar ta yi masa, ya kara da cewa gaggawar zuwan da yan sanda suka yi ya ceci ran amaryar domin mutanen unguwa sun fara dukanta.

Ya ce 'yan sanda sun kama wacce ake zargin.

Dukkan kokarin ji ta bakin yan sanda bai yiwu ba domin kakakin yan sandan bai daga wayansa ba kuma bai amsa sakon kar ta kwana ba.

Kano: Mata ta garzaya kotun shari'a ta nemi a raba aurenta da mijinta saboda murguɗa baki

A wani labarin, mata ta maka mijin ta gaban kotu don bukatar a raba auren su sakamakon yadda rikici da tashin hankali ke aukuwa tsakanin su.

Ta bayyana gaban Alkali Munzali Tanko na kotun musulunci da ke zama a Kofar Kudu a birnin Kano don gabatar da korafin ta bisa ruwayar Dala FM.

Kamar yadda ta ce, mijin na ta ya na ci wa iyayen ta mutunci kuma ba ya ganin darajar su ko kadan kamar yadda ya zo a ruwayar na Dala FM.

Asali: Legit.ng

Online view pixel