Magidanci ya nemi kotu ta raba auren shekaru 19 saboda matarsa na 'sheƙe aya' da mai maganin gargajiya

Magidanci ya nemi kotu ta raba auren shekaru 19 saboda matarsa na 'sheƙe aya' da mai maganin gargajiya

  • A ranar Alhamis wata kotu da ke zama a Ado-Ekiti ta warware wani aure mai shekaru 19 tsakanin Adeniyi Adeyemi dan shekara 72 da Folasade, matarsa mai shekaru 52
  • An raba auren ne akan zargin rashin hakuri, lalata da kuma rashin kamun kai inda mijin ya ce Folasade ta na da taurin kai kuma har lalata ta ke yi da wani mai maganin gargajiya
  • Ya bayyana wa kotu yadda ya fuskanci mutumin da ta ke lalata da shi wanda ya yi masa alkawari yanke alaka da matarsa amma abin ya ci tura, sai ma ci gaba su ka yi

Jihar Ekiti - Wata kotu da ke zama a Ado-Ekiti ta raba wani aure mai shekaru 19 a ranar Alhamis tsakanin Adeniyi Adeyemi mai shekaru 72 da matarsa, Folasade.

Kara karanta wannan

Dan Najeriya ya maka MTN a kotu kan cire masa N50, an biya shi N5.5m diyya

Premium Times ta rahoto yadda mijin ya sanar da kotu yadda Folasade ta ke da taurin kai, rashin hakuri da kuma rashin kamun kai sakamakon sheke ayar da take yi da wani mai maganin gargajiya.

Magidanci ya nemi kotu ta raba auren shekaru 19 saboda matarsa na 'sheƙe aya' da mai maganin gargajiya
Wani mutum ya nemi kotu ta raba auren shekaru 19 saboda matarsa na 'sheƙe aya' da mai maganin gargajiya. Hoto: Premium Times
Asali: Facebook

Shin kana da labarin da ka/ki ke son an wallafa ma ka/ki? Ka tuntubemu a info@corp.legit.ng!

Ya bayyana wa kotu cewa har fuskantar mai maganin gargajiyar ya yi wanda ya yi masa alkawarin rabuwa da matar amma ya ki, Premium Times ta ruwaito.

Adeyemi, mahaifin yara 2 ya kuma zargi matarsa da fita ba bisa izininsa ba inda ta yi makwanni 2 ba tare da ya sani ba kuma ko nadama ba ta yi ba.

Ya bukaci kotu ta raba aurensu kuma ta ba shi damar rike yaransu, namiji mai shekaru 18 da mace mai shekaru 15.

Folasade ta musanta zargin

A bangaren ta, Folasade ta musanta zargin da mijinta ya ke yi mata.

Kara karanta wannan

Rikicin VAT: Gwamnatin Buhari na tunanin sasantawa da Wike da Gwamnonin Kudu ta huta

Inda ta ce kishiyarta ce ta kumbura mata hannunta, hakan ya sa ta nemi taimakon mai maganin gargajiya.

A cewarta yayanta ne ya tura ta wurin mai maganin sannan ta ce babu wata alakar da ke tsakaninta da mutumin.

Ta zargi mijinta da auna wa yaranta da ita zagi yadda ya ga dama, don haka ta amince da rabuwar auren nasu.

Alkalin ya raba auren take yanke

Alkalin kotun, Olayinka Akomolede ta duba yadda auren ya lalace don haka ta raba auren nasu.

Akomolede ta ba Folasade damar rike diyarta mace yayin da ta bukaci dan namiji ya zaba wanda ya ke son zama da shi cikin iyayen.

Har ila yau, alkalin ya umarci Adeyemi da daukar nauyin karatun yaran sannan ya dinga ba diyarsa N10,000 duk wata a matsayin kudin ciyarwa.

Kano: Mata ta garzaya kotun shari'a ta nemi a raba aurenta da mijinta saboda murguɗa baki

A wani labarin, mata ta maka mijin ta gaban kotu don bukatar a raba auren su sakamakon yadda rikici da tashin hankali ke aukuwa tsakanin su.

Kara karanta wannan

Rahoton EndSARS: HURIWA ta bukaci Buhari ya fatattaki Lai Mohammed kan karyar da ya zuga

Ta bayyana gaban Alkali Munzali Tanko na kotun musulunci da ke zama a Kofar Kudu a birnin Kano don gabatar da korafin ta bisa ruwayar Dala FM.

Kamar yadda ta ce, mijin na ta ya na ci wa iyayen ta mutunci kuma ba ya ganin darajar su ko kadan kamar yadda ya zo a ruwayar na Dala FM.

Asali: Legit.ng

Online view pixel