An zabi Aisha Buhari a matsayin shugaba a kungiyar matan shugabannin kasashen Afrika

An zabi Aisha Buhari a matsayin shugaba a kungiyar matan shugabannin kasashen Afrika

  • Aisha Buhari ta zama shugaba a kungiyar matan shugabannin kasashen Afrika masu fafatukar wanzar da zaman lafiya
  • Hakan na zuwa ne jim kadan bayan da ta karbi bakuncin matan shugabannin kasashen na Afrika a wani taron kungiyar
  • Aisha Buhari ta bayyana manufofinta, tare da kudurta aiki tukuru da gaskiya da jajircewa har ma da rikon amana

Abuja - Aisha Buhari ta zama shugabar matan shugabannin kasa masu fafatukar wanzar da zaman lafiya a Afirka, gidan talabijin na Channels ya ruwaito.

Babban taro karo na 9 na kungiyar matan shugabannin kasashen Afrika ta AFLPM ya zabi uwargidan shugaban kasar Najeriya Aisha Buhari a matsayin sabuwar shugabar kungiyar.

Hakan na kunshe ne cikin wata sanarwa da mai baiwa shugaban kasa shawara kan harkokin yada labarai Femi Adesina ya sanyawa hannu ranar Litinin 22 ga watan Nuwamba a Abuja.

Kara karanta wannan

Labari da Hotuna: Yadda mata zasu iya taka rawar gani wajen tabbatar da zaman lafiya, Shugaba Buhari

Uwargidan shugaban Najeriya
An zabi Aisha Buhari a matsayin shugaba a kungiyar matan shugabannin kasashen Afrika | Hoto: channelstv.com
Asali: Depositphotos

Shugaban kasa Muhammadu Buhari wanda ya bayyana bude taron ya taya uwargidan nasa murnar samun fili a madadin dukkan matan shugabannin Afrika domin bunkasa sakateriyar kungiyar da ke Abuja.

Shin kana da labarin da ka/ki ke son an wallafa ma ka/ki? Ka tuntubemu a info@corp.legit.ng!

Aisha a jawabinta na nadin, ta yi alkawarin sauke nauyin da aka dora mata tare da jajircewa, inda ta bukaci takwarorinta da su yi aiki tare domin samun makoma mai kyau ga Afirka.

A kalamanta:

"Da dukkan girnamawa, na amince da zabena a matsayin shugaba ta 9 mai jiran gado na tawagar matan shugabannin kasashen Afirka.
“Ina so na gode wa dukkan takwarorina bisa ga ci gaba da goyon baya da fahimta da suka ba ni wannan babban nauyi.
"Na yi alkawarin aiwatar da aiki na tare da cikakken himma kuma bisa ga ka'idodin da aka gindaya.
“Shugabanni da ‘yan jarida, kamar yadda kuka sani, aikin da ke gabanmu aiki ne na gama-gari, don haka ana bukatar hadin kan mu baki daya domin samun nasarar aikin wanzar da zaman lafiya na matan shugabannin Afirka baki daya.

Kara karanta wannan

Aisha Buhari ta karbi bakuncin matan shugabannin kasashen Afrika a wata ziyara

“A nawa bangaren, ina mai tabbatar muku da cewa zan sauke al’amuran ofishina da gaskiya, sadaukarwa, da kuma hada kai.
“Ya ku abokan aikina yayin da muke kammala wannan taro, ya kamata tarihi ya jagorance mu don ganin cewa Afirka da za mu bar wa ’ya’yanmu a yau ta fi wacce muka gada.
"Ya kamata mu sadaukar da kanmu don yin aiki tare don cimma kyakkyawar makoma ga dukkan 'yan Afirka.'

Aisha Buhari ta karbi bakuncin matan shugabannin kasashen Afrika a Abuja

A tun farko, uwargidan shugaban kasan Najeriya Aisha Buhari a ranar Lahadi ta karbi bakuncin takwarorinta na kasashen Saliyo, Congo Brazzaville, Sao Tome a da Principe a wata ziyara.

Hakazalika, ta karba har da wakilan kasashen Zimbabwe, Cote D`voire da Mauritania gabanin taron koli karo na 9 na tawagar wanzar da zaman lafiya ta matan shugabannin Afirka (AFLPM).

NAN ta ruwaito cewa, wadanda suka iso su ne Maria de Fatima Vila Nova, ta Sao Tome da Principe, Antoinette Sassou Nguesso, ta Congo Brazzaville da Fatima Maada Bio, ta Saliyo.

Kara karanta wannan

Shugabancin 2023: Ku jira don jin ta bakinsa a watan Janairu - Fashola game da takarar Tinubu

Asali: Legit.ng

Online view pixel