Shugabancin 2023: Ku jira don jin ta bakinsa a watan Janairu - Fashola game da takarar Tinubu

Shugabancin 2023: Ku jira don jin ta bakinsa a watan Janairu - Fashola game da takarar Tinubu

  • Ministan ayyuka da gidaje, Babatunde Fashola, ya magantu a kan rade-radin takarar shugabancin jagoran APC, Tinubu a zaben shugaban kasa na 2023
  • Fashola ya bukaci 'yan Najeriya da su saurara har zuwa watan Janairu 2022 domin jin gaskiyar lamari daga bakin babban jagoran na APC na kasa
  • Ya ce tsohon gwamnan na Lagas bai sanar da shi kan ko zai yi takarar kujerar ba a lokacin da suka hadu a makon da ya gabata

Ministan ayyuka da gidaje, Babatunde Fashola, ya bukaci 'yan Najeriya da su saurara har zuwa watan Janairu 2022 domin jin ta bakin jagoran jam'iyyar All Progressives Congress na kasa, Bola Tinubu, kan ko zai yi takarar shugaban kasa a 2023 ko a'a.

Fashola ya bayyana hakan ne a wani shirin Channels TV a ranar Juma'a, 19 ga watan Nuwamba wanda jaridar Punch ta sanya ido.

Kara karanta wannan

Yakin neman zaben Tinubu ya shigo yankin Arewa, Matasa su na goyon bayan shi a Filato

Shugabancin 2023: Ku jira don jin ta bakinsa a watan Janairu - Fashola game da takarar Tinubu
Shugabancin 2023: Ku jira don jin ta bakinsa a watan Janairu - Fashola game da takarar Tinubu Hoto: Today.ng
Asali: UGC

A yan baya-bayan nan, an gano fastocin Tinubu inda ake rade-radin yana neman takarar kujerar shugaban kasa a manyan birane ciki harda Lagas da Abuja.

Koda dai Tinubu bai fito ya ayyana aniyarsa na takarar kujerar ba a 2023, akwai rahotanni da alamu da ke nuna cewa watakila yana da ra'ayin neman kujerar ta daya a kasar.

Shin kana da labarin da ka/ki ke son an wallafa ma ka/ki? Ka tuntubemu a info@corp.legit.ng!

Wasu kungiyoyi da mutane sun kuma bayyana cewa baya ga Tinubu, mataimakin shugaban kasa, Yemi Osinbajo, gwamnan jihar Ekiti, Kayode Fayemi, da Fashola za su iya rike Najeriya.

Da aka tambaye shi kan ko yana da ra'ayin zama shugaban kasar Najeriya, Fashola ya ce:

"Babban aiki ne, mai matukar wahala; bana yiwa wadanda suka riki mukamin bakin ciki kuma bana yi wa wadanda ke takara bakin cikin samun shi."

Kan ko zai yi magana da yawun wani dan takara a 2023, ministan ya ce:

Kara karanta wannan

Da dumi-duminsa: Shugabannin Igbo sun gana da Buhari a fadar Villa

"A iya sani na, babu wanda ya fadi cewa, 'ina so na zama shugaban kasar Najeriya'. Akwai mutanen da ke ciwa mutane albasa. Babu wanda ya fito, Ba mu kai wannan matakin ba tukuna.
"Ina iya fitowa na ce zan yi magana da yawun wane ko wane. Ku bari mai shi ya fito ya fadi da bakinsa, 'ina so na yiwa Najeriya hidima.'
"Yana yi mun ciwo wasu lokutan idan muka ga cewa muhimmin aiki da hakki ya zama, 'mutane na sun ce'. Ina ganin zai fi dacewa abun ya zama zan iya, na dubi kaina, ku bani matsalarku, ku kuje kuyi bacci'."

Kan ko zai marawa takarar shugabancin Tinubu na 2023 da ake ta rade-radi, tsohon gwamnan na Lagas ya ce:

"Na gan shi a makon da ya gabata, bai fada mani cewa zai yi takarar kujera ba kuma a iya sanina a jawabin karshe da yayi a kai ya ce mutane za su sani a watan Janairu."

Kara karanta wannan

Kungiyar 'Edo Volunteers for Tinubu 2023' tana goyon bayan ƙusan APC a zaben 2023

Fashola ya kuma ce bai tambayi Tinubu kan ko yana da ra'ayin takarar shugaban kasa a 2023 ko bai da ra'ayi ba.

"A'a, ban tambaye shi ba, Kawai na je na tambayi yaya yake ne. Ya fitar da jawabin cewa 'Zan yi magana a watan Janairu,' don haka mu jira har zuwa watan Janairu."

2023: Tinubu ya samu gagarumin goyon bayan sarakuna 300 domin ya gaji kujerar Buhari

A gefe guda, mun ji cewa akalla sarakunan gargajiya sama da 300 daga kudu maso yamma ne ke goyon bayan takarar tsohon gwamnan jihar Lagas, Sanata Bola Tinubu, a zaben shugaban kasa na 2023.

Sanata Dayo Adeyeye, shugaban kungiyar yakin neman zaben Tinubu ne ya bayyana hakan a Gbongan, jihar Osun, rahoton Punch.

Ya bayyana hakan ne yayin kaddamar da kungiyar mai suna ‘South West Agenda for Asiwaju for 2023’ a mazabar Irewole.

Asali: Legit.ng

Online view pixel