Labari da Hotuna: Yadda mata zasu iya bada gudummuwarsu wajen tabbatar da zaman lafiya, Shugaba Buhari

Labari da Hotuna: Yadda mata zasu iya bada gudummuwarsu wajen tabbatar da zaman lafiya, Shugaba Buhari

  • Shugaba Muhammadu Buhari yace mata na da gudummuwar da zasu bada sosai wajen sake gina zaman lafiya a nahiyar Afirka
  • Buhari ya kuma jawo hankalin shugabannin Afirka da kuma masu ruwa da tsaki su tallafawa mata domin gina al'umma mai son zaman lafiya
  • Aisha Buhari, wacce aka zaɓa sabuwar shugabar kungiyar matan shugabannin, tace zata yi iya bakin kokarinta

Abuja - Shugaban ƙasa, Muhammadu Buhari, ya nuna goyon bayansa kan kudirin matan shugabannin kasashen Afirka, AFLPM, wanda zai maida hankali kan tabbatar da zaman lafiya da kawo cigaba a nahiyar.

Da yake jawabi a wurin buɗe taron karo na 9, Buhari ya roki shugabannin kasashen Afirka da masu ruwa da tsaki su tallafa wa matan wajen gina al'umma masu zaman lafiya.

Shugaban ƙasan ya nuna damuwarsa kan yadda zaman lafiya ya kubce kuma ya jawo nakasu a ɓangaren cigaba na kasashen Afirka da dama.

Kara karanta wannan

Dalilin da yasa mutanen kirki ba su shiga siyasa a Najeriya, Gwamna Masari

Taron mata
Labari da Hotuna: Yadda mata zasu iya bada gudummuwarsu wajen tabbatar da zaman lafiya, Shugaba Buhari Hoto: Buhari Sallau
Asali: Facebook

A jawabin da Femi Adesina ya fitar a Facebook, Buhari yace:

"Ayyukan yan ta'adda da yan fashin daji ya jawo mutane da dama sun bar gidajensu, kuma ya jefa wasu cikin kangin talauci."
"Babu tantama mata da kananan yara ne wannan matsalar ta fi yiwa illa. Saboda haka a matsayin ku na iyaye mata, na yi imanin cewa kuna da rawar da zaku taka wajen sake gina zaman lafiya."
"Naji daɗin sanin cewa kungiyar ku tana aiki ba dare ba rana wajen samar da ingantaccen zaman lafiya a kasashen mu na Afirka ta hanyoyi daban-daban."

Buhari ya yaba wa matarsa, Dakta Aisha Buhari, bisa kokarin da ta yi na samun wuri a madadin sauran matan shugabannin Afirka domin gina sakateriyar su a Abuja.

Kara karanta wannan

Bukatar sakin Nnamdi Kanu babban lamari ne, amma zan yi shawara: Buhari ga Dattawan Igbo

"Naji daɗi da nasan cewa sakateriyar idan aka kammala zata yi aiki da dama da suka haɗa da samar da ayyukan yi da kuma kuɗaɗen shiga."
Taron mata
Labari da Hotuna: Yadda mata zasu iya bada gudummuwarsu wajen tabbatar da zaman lafiya, Shugaba Buhari Hoto: Buhari Sallau
Asali: Facebook

Matan sun zabi Aisha Buhari a matsayin shugaba

Taron kungiyar matan AFLPM karo na 9, ba tare da hamayya ba ya zaɓi matar shugaban Najeriya a matsayin shugabar kungiya.

A jawabinta, Aisha Buhari, ta sha alwashin sadaukar da kanta wajen sauke nauyin da aka ɗora mata, tare da rokon abokan aikinta su yi aiki cikin haɗin kai.

Aisha tace:

"Na amince da zaɓe na da aka yi a matsayin shugaban kungiyar matan shugabannin kasashen Afirka ta 9, kuma ina mika godiya ta ga abokan aiki da suka amince da ɗora mun wannan nauyin."
"Zan yi iyakar kokarina wajen sauke nauyin da aka ɗora mun, ta hanyar sadaukarwa da kuma bin dokoki."
"Ta bangare na ina mai tabbatar muku da cewa zan gudanar da ayyukan ofishina da gaskiya, sadaukarwa kuma ba tare da nuna banbanci ba."

Kara karanta wannan

Shugaban Najeriya Buhari zai ba Gwamnoni 36 bashin Naira Biliyan 650 da za a karba a 2051

Taron matan Afirka
Labari da Hotuna: Yadda mata zasu iya bada gudummuwarsu wajen tabbatar da zaman lafiya, Shugaba Buhari Hoto: Buhari Sallau
Asali: Facebook

Taron matan Afirka
Labari da Hotuna: Yadda mata zasu iya bada gudummuwarsu wajen tabbatar da zaman lafiya, Shugaba Buhari Hoto: Buhari Sallau
Asali: Facebook

A wani labarin na daban kuma Jerin matakan da zaka bi, kamallaki gida a saukake a shirin cefanar da gidaje na FG

A ranar Jumu'a da ta gabata, 12 ga watan Nuwamba, gwamnatin tarayya ta kaddamar da shirin siyar da gidajen da ta gina ga yan Najeriya a farashi mai rahusa.

Gwamnatin ta bude sabon shafin yanar gizo domin mutane su nemi siyan ɗaya daga cikin gidajen kai tsaye daga inda suke.Mun tattara muku jerin hanyoyin da zaku bi, ku cike bayanan ku a wannan shafin domin amfana da shirin.

Asali: Legit.ng

Online view pixel