Aisha Buhari ta karbi bakuncin matan shugabannin kasashen Afrika a Abuja

Aisha Buhari ta karbi bakuncin matan shugabannin kasashen Afrika a Abuja

  • Uwargidan shugaban kasa ta karbi bakuncin wasu jiga-jigan matan shugabannin kasa a Afrika a jiya Lahadi
  • Aisha Buhari ta karbe su a Abuja gabanin wani taron zaman lafiya da za a gudanar na matan shugabannin Afrika
  • Ya zuwa yanzu, wasu daga ciki basu iso ba, ana sa ran isowar matan shuganannin kasashen Ghana da sauransu

Abuja - Uwargidan shugaban kasan Najeriya Aisha Buhari a ranar Lahadi ta karbi bakuncin takwarorinta na kasashen Saliyo, Congo Brazzaville, Sao Tome a da Principe a wata ziyara.

Hakazalika, ta karba har da wakilan kasashen Zimbabwe, Cote D`voire da Mauritania gabanin taron koli karo na 9 na tawagar wanzar da zaman lafiya ta matan shugabannin Afirka (AFLPM).

Aisha Buhari ta karbi bakuncin matan shugabannin kasashen Afrika a Abuja
Aisha Buhari, uwargidan shugaban kasa | Hoto: guardian.ng
Source: UGC

NAN ta ruwaito cewa, wadanda suka iso su ne Maria de Fatima Vila Nova, ta Sao Tome da Principe, Antoinette Sassou Nguesso, ta Congo Brazzaville da Fatima Maada Bio, ta Saliyo.

Read also

Jigon APC ya bayyana sirri, ya ce Buhari na goyon bayan shugaba daga yankin Igbo

Aisha Buhari ta kuma karbi bakuncin wakilan matan shugabannin kasashen Cote D’voire, Mouritania da Zimbabwe.

Shin kana da labarin da ka/ki ke son an wallafa ma ka/ki? Ka tuntubemu a info@corp.legit.ng!

Aisha, wacce ta yi maraba da matan shugabannin kasan da suka kawo ziyara Najeriya, ta bayyana jin dadinta da zuwansu.

Ana sa ran halartar matan shugabannin kasashen Ghana, Laberiya, Nijar, Namibiya, da dai sauransu, kamar yadda Premium Times ta ruwaito.

Aisha Buhari ta bayyana burinta na tallafawa mata da kananan yara su samu ilimi

A wani labarin, Daily Nigerian ta ruwaito cewa, uwargidan shugaban kasa, Aisha Buhari, ta bayyana cewa a shirye ta ke ta karfafa hadin gwiwa da sauran masu hannu da shuni don bayar da tallafin da ake bukata a ci gaban ilimin mata da yara.

Aisha Buhari ta bayyana haka ne a ranar Alhamis, a lokacin da ta karbi bakuncin mambobin kungiyar masu harhada magunguna ta Najeriya (NAPPSA), daga kasar Amurka, wadanda suka kai mata ziyara a Abuja.

Read also

Tinubu ya bayyana dalilin da yasa ya ziyarci Orji Kalu a Abuja

Ta ce gidauniyar ta, ta hanyar hadin guiwar abokan huldar ci gaba, ta bayar da tallafi ga mata, matasa da sauran iyalai marasa galihu, musamman a fannin kiwon lafiya, gina asibitocin haihuwa da inganta ilimin yara mata.

Source: Legit.ng

Online view pixel