'Yar Sarkin Kano Sanusi: Na gwammace ɓarawo ya sace kuɗin da in bawa miji na N500,000 ya ƙara aure

'Yar Sarkin Kano Sanusi: Na gwammace ɓarawo ya sace kuɗin da in bawa miji na N500,000 ya ƙara aure

  • Yar Sarkin Kano na 14 , Sanusi Lamido Sanusi, Shahida ta bayyana cewa ta gwammace barawo ya sace mata N500,000 da ta bawa mijinta ya kara aure
  • Shahida ta bayyana hakan ne yayin da ta ke bada amsa game da tambayar da aka yi a Instagram ga mata game da bawa miji kudi ya kara aure
  • A cewar ta idan barawo ya sace kudin tamkar sadaka ta yi kuma akwai yiwuwar ta samu abinda ya fi N500,000 a gaba idan ta yi hakuri

Shahida, yar Sarkin Kano na 14, Sanusi Lamido Sanusi, tace ta gwammace barayi su sace mata N500,000 a maimakon ta bawa mijinta kudin ya kara cikin gara domin auro mata kishiya.

Mahaifiyar 'ya'ya biyun ta bayyana hakan ne a ranar Lahadi, 21 ga watan Nuwamban 2021, yayin da ta ke martani kan wata wallafa da aka yi a shafin Instagram.

Read also

Bayan shekaru 5 da ɓatan ɗiyarsa, mahaifi ya rubuta wasiƙa mai taɓa zuciya

'Yar Sarkin Kano Sanusi: Na gwammace ɓarawo ya sace kuɗin da in bawa miji na N500,000 ya ƙara aure
'Yar Sarkin Kano: Na gwammace ɓarawo ya sace kuɗin da in bawa miji na N500,000 ya ƙara aure. Hoto: Sheyheels
Source: Instagram

'Yar Sarkin Kano Sanusi: Na gwammace ɓarawo ya sace kuɗin da in bawa miji na N500,000 ya ƙara aure
'Yar Sarkin Kano Sanusi II: Na gwammace ɓarawo ya sace kuɗin da in bawa miji na N500,000 ya ƙara aure. Hoto: @yourbusinesshive
Source: Instagram

Wallafar ya ce:

"Wannan na mata ne. Kina da N500k, za ki bawa mijin ki a matsayin gudunmawa domin ya kara mata ta biyu ko kuma kin gwammace a sace kudin"

A yayin da ta ke bada amsa, Shahida ta rubuta:

"Ba dai sata kadai bane? Babu wanda za a yi wa rauni ko? Zan samu lada ma idan hakan ya faru, wata kila ma in samu ninkin kudin idan na yi hakuri."

Ma'ana dai Shahida ta gwammace barawo ya sace zunzurutun kudin, N500,000 a maimakon ta bawa mijinta ya kara aure.

Martanin wasu matan game da tambayar

aqeeba ta ce:

"Na fara rubuta cewa 'gara in saka kudin a masai' sai kuma na sake tunani'.... 'ya danganta da yanayin', sai kuma tambayar ya bani haushi ma, bai dace in bata raina ba tunda safe."

Read also

Magidanci ya nemi kotu ta raba auren shekaru 19 saboda matarsa na 'sheƙe aya' da mai maganin gargajiya

aiisha_tahir ta ce:

"Gara barawon ya sace kudin ko ba komai zan samu lada a ranar lahira".

women_parlour_gyaran_aure cewa ta yi:

"A'a, sai dai idan dalilin daga ni ne na kara auren, watakila banda lafiya ko wani dalilin."

_hanifatu ta amsa da cewa:

"Zan bada gudumawar tunda kishiya ba abokiyar gaba bane."

ita kuma ddjumare cewa ta yi:

"Wannan wane irin tambaya ne don Allah"

Zugar Ƙawaye Na Bi: Ku Taya Ni Roƙon Mijina Ya Mayar Da Ni, Tsohuwar Matar Babban Sarki a Najeriya

A wani labarin, jun ji cewa Olori Damilola, tsohuwar matar Alaafin na Oyo, Oba Lamidi Adeyemi ta fito fili ta bai wa basaraken da gidan sarautar hakuri.

A wata takarda wacce ta wallafa ta shafin ta na Instagram a ranar Lahadi, sarauniyar ta bai wa gabadaya ‘yan uwan Adeyemi hakuri da kuma majalisar jihar Oyo.

Damilola, wacce ita ce amaryar basaraken, ta zargi gidan sarautar da nuna halin ko-in-kula akan ta da dan ta daya tal.

Read also

Yajin aikin ASUU: FG za ta rabawa jami’o’i biliyan N22.72 a ranar Laraba – Ministan Buhari

Source: Legit.ng

Online view pixel