Zugar Ƙawaye Na Bi: Ku Taya Ni Roƙon Mijina Ya Mayar Da Ni, Tsohuwar Matar Babban Sarki a Najeriya

Zugar Ƙawaye Na Bi: Ku Taya Ni Roƙon Mijina Ya Mayar Da Ni, Tsohuwar Matar Babban Sarki a Najeriya

  • Sarauniya Damilola, tsohuwar matar Alaafin na Oyo, Oba Lamido Adeyemi ta bai wa basaraken da kuma gabadaya gidan sarautar hakuri ta shafin ta na Instagram
  • Damilola ta fito karara inda ta karyata kan ta da kan ta, ta ce zugar kawaye ce ta sa ta shirya karairayi dangane da basaraken kuma yanzu ta gane kuskuren ta
  • Dama a kwanakin baya ta ce abinda ya sa ta bar gidan sarautar shi ne yadda basaraken ya ke nuna halin ko-in-kula akan ta da dan ta, yanzu duk ta karyata kan ta

Jihar Oyo - Olori Damilola, tsohuwar matar Alaafin na Oyo, Oba Lamidi Adeyemi ta fito fili ta bai wa basaraken da gidan sarautar hakuri.

A wata takarda wacce ta wallafa ta shafin ta na Instagram a ranar Lahadi, sarauniyar ta bai wa gabadaya ‘yan uwan Adeyemi hakuri da kuma majalisar jihar Oyo.

Kara karanta wannan

Ba ni da hannu a dirar mikiya da jami'an tsaro suka yi a gidan Mary Odili, Malami

Zugar Ƙawaye Na Bi: Ku Taya Ni Roƙon Mijina Ya Mayar Da Ni, Tsohuwar Matar Babban Sarki a Najeriya
Zugar Ƙawaye Na Bi: Ku Taya Ni Roƙon Mijina Ya Mayar Da Ni, Tsohuwar Matar Babban Sarki a Najeriya
Asali: Instagram

Damilola, wacce ita ce amaryar basaraken, ta zargi gidan sarautar da nuna halin ko-in-kula akan ta da dan ta daya tal.

A yanzu kuwa ta ce ta gane kuskuren ta kuma ta bukaci gaba daya gidan su yafe mata inda ta ce zuga ta aka yi.

Kamar yadda ta wallafa:

“Ina so kowa ya fahimce ni, ba kawai na yi wannan rubutun haka nan bane, sai dai akan abinda ya shafe ni ne kwarai.
“Ina so in bayyana cewa duk ba gaskiya bane abinda na fadi akan fada kuma da na ce sarki be damu da ni ba shiyasa na bar fadar, ba gaskiya ba ne.
“Kawaye na ne su ka zuga ni, ba da son rai na na yi hakan ba.”

Kara karanta wannan

Funmilayo Ransome-Kuti: Abubuwa 4 game da macen da ta fara tuka mota a Najeriya

Ta ce yanzu idon ta ya bude

Damilola ta kara da cewa yanzu idanun ta sun bude.

“Ina rokon duk wata uwa a duniyar nan da ta taimaka ta roki miji na ya mayar da ni.”

A karkashin wallafar ta kara da cewa:

“Mai wayau ne kadai zai fahimci cewa kowa ya bar gida, gida ya bar shi.”

Bayan rayuwa cikin daji yana cin ciyawa, yanzu wankan sutturu na alfarma ya ke yi, ana girmama shi a gari

A wani rahoton, wani matashi, Nsanzimana Elie ya kasance a baya ya na zama cikin daji saboda yanayin suffar sa, sannan mutanen kauyen sa har tonon sa su ke yi.

Akwai wadanda su ke kiran sa da biri, ashe daukaka ta na nan biye da shi, kamar yadda Legit.ng ta ruwaito.

Mahaifiyar Elie ta ce Ubangiji ya amshi addu’ar ta na ba ta shi da ya yi bayan yaran ta 5 duk sun rasu, kuma ba ta kunyar nuna shi.

Asali: Legit.ng

Online view pixel